Daga Pauline Odhiambo
Wani ɗan kasar Kenya mai ƙirƙire-ƙirƙire kana ɗan kasuwa Kenya James Muritu ya bayyana nasarar sakamakon ''gwajin kimiyyar'' da ya yi, bayan da ya samu wata hanya ta musamman wajen sarrafa sharar rabobi zuwa man fetur a yayin aikin gwajin narkar da rabobin da za a yi amfani da su don ginda hanyoyi.
''Na kasance ina haɗa tulaban gini daga sharar rabobi kuma a lokacin da na ke gwaje-gwajena, na ga ruwa daga robobin da ke narkewa yana kamawa da wuta. Hakan ya matukar janyo hankali," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika
Binciken ya sa James ya yi watsi da aikin da yake yi kana ya mayar da hankali ga samar da mai - canjin da ya samu a 2023 lokacin da ya sarrafa mai daga sharar robobi da ya kona mai zafi.
Ya cim ma hakan ne ta hanyar tsarin Pyrolysis, wato ƙona rabbobi da wuta mai tsananin zafi.
''Da zarar na sarrafa man fetur din, sai na gwada a cikin injinan janareta daban-daban don tantance amfaninsa wajen samar da wutar lantarki,'' in ji James, wanda ya kafa kamfanin Progreen Innovations da ya ƙware wajen mayar da sharar robobi zuwa man fetur.
"Na kuma gwada man a cikin injin ɗin aikin gona, kuma ya yi aiki sosai."
Tsari mara gurɓatarwa
An lissafa ƙirkirar da James ya yi cikin dubban ayyuka a duniya waɗanda ke kokarin magance matsalar sharar rorobi a duniya.
Bayanan da Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) ta tattara sun nuna cewa a duk shekara ana samar da sharar robobi har kusan tan miliyan 400 a duk duniya.
Kasa da kashi 10 cikin dari na wannan sharar ne kawai ake sake sarrafawa, yayin da a bangare guda ake ƙona kashi 12 cikin 100.
Mafi yawan sauran sharar robobin, ana jibge su a wuraren zubar da bola, inda ake kwashe ɗaruruwan shekaru kafin su narke gaba ɗaya.
James da tawagarsa suna tattara sharar robobi iri daban-daban, waɗanda suke tacewa da kuma tsaftace su kafin a yayyanka su.
Ana zuba rabobin da aka yayyanka cikin wata na'ura da ke hana fitar iskar Oxygen wadda za ta sarrafa su zuwa mai a cikin tsari mara hayaki. Ana amfani samfurin sinadarin "biochar" don rura wutar nau'rar.
Baki ɗaya tsarin na ɗaukar awanni 24 zuwa 36, ya dai danganta da nauyin robar da aka saka a cikin na'urar.
"Abin da muke ya saɓa da tsarin yadda ake ƙonawa," kamar yadda James ya bayyana wa TRT Afrika.
"Tsarin ƙonawar, yana fitar da hayaki sosai, sannan gubar warin hayakin kan cika iskar da ake shaƙa,'' in ji James
Ya kuma ƙara da cewa ''Babu wata gurbatacciyar iska da ke fita a namu irin aikin, kuma muna ci gaba da bincike don tabbatar da cewa ba a samu sinadarin carbon 100 bisa 100 ba."
Ƙananan robobi da ake amfani da su wajen sarrafa gorar ruwa da kwanon abinci, ba su dace da waɗanda ake buƙata wajen samar da man fetur ba saboda sinadaran da aka yi mafani wajen sarrafa su.
Don haka, kamfanin James ya cire ire-iren robobin daga tsarin ayyukansa.
Zaɓin man fetur mai rahusa
Ana samar da danyen mai ne a matakin farko a yayin sarrafa shi sannan a tace zuwa man fetur da diezal.
Za a iya amfani da madadin man a cikin ƙanana da matsakaicin injina masu amfani da mai, yayin dizel kuma a cikin manyan janareta da injuna masu nauyi.
Kazalika James na amfani da man diezal ɗin ya sarrafa a motarsa wanda yake amfani da ita wajen ɗaukar kayayyakin kasuwancinsa.
A yanzu haka dai tsarin Progreen Innovations na samar da man fetur har zuwa lita 1,000 a kowane mako.
Yawanci dai masu tuka motoci da ke jigilar kayayyaki masu nauyi ne suka fi sayen man dizel din.
Wani abokin cinikin James na sayan man diezal din don aikin manyan motocin da ake amfani da su wajen tono da kera hanyoyi.
Masu sana'ar tuka babura ne suka fi sayan man fetur din da James ke sarrafawa wanɗa aka saninsa da boda boda.
"Ingancin kayanmu shi ne ana iya hada shi da man fetur ko dizel da ake samu daga gidajen mai,'' in ji James, wanda ke kokarin kara yawan adadin da kamfaninsa ke samarwa zuwa lita 20,000 a duk mako.
"Masu amfani da man Boda suna sayen man da na sarrafa saboda araharsa idan aka kwatanta da sauran man da ake hadawa, bayanai da muke samu shi ne, suna iya yin aiki na tsawon lokuta tare da tara kudin man.''
Kalubalen kuɗi
Sai da James ya kwashe shekara guda kafin ya samu izini daga sashen tantance ingancin kayayyaki na kasar Kenya don sayar da kuma rarraba kayayyakinsa.
A yanzu haka dai James ya dogara ne da ƙudin aljihunsa, musamman kan albashinsa a matsayinsa na masanin kimiyyar fasaha don ɗaurewar kasuwanci.
"Yawan shakku game da samfurin man da nake sarrafawa na zama cikas. Mutane da dama ba su yarda da wata hanyar samun man fetur ko diezal ba face daga gidajen mai da aka saba gani," in ji James.
Amma duk da waɗannan ƙalubalen, har yanzu yana samun lokacin horar da ɗaliban injiniyanci.
A kai a kai yana karɓar baƙuncin ƙungiyoyi daga jami'o'in cikin gida, yana ƙarfafa musu gwiwar ƙirkire-ƙirkire.