Ambaliyar Maiduguri

Daga Halima Umar Saleh

Ambaliyar ruwa ba sabon iftila’I ba ne, lamari ne da aka saba gani a sassa daban-daban a fadin duniya.

Amma kuma tun da ba a sabo da wahala, to a koyaushe ta faru hankula kan tashi saboda irin ɓarna da mummunan tasirin da take yi a kan rayuka da zamantakewa da tattalin arziki.

Daga nahiyar Amurka zuwa ta Turai, Asiya zuwa Australiya har aka gangaro zuwa Afirka, ambaliya kan afku daga lokaci zuwa lokaci sakamakon abubuwa da dama, ciki har da na sauyin yanayi.

Shekarar 2024 kamar shekarun baya-bayan nan ta zo da bala’in ambaliyar ruwa, musamman a nahiyar Afirka da Asiya, inda lamarin ya fi shafar ƙasashe irinsu Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da Guinea da Laberiya da Mali da Pakistan da Bangaladesh da Indiya da sauran su.

Hukumomi sun ce bala’in ya shafi miliyoyin mutane, ya yi sanadin mutuwa dubbai, ya kuma ɗaiɗaita wasu dubban da raba su da muhallansu.

Duk da irin alwashin da gwamnatoci da hukumomi da ma masu ruwa da tsaki ke ɗauka na magance sake afkuwar ambaliya a wuraren da ake yawan yi, wasu na ganin tamkar matakan da ake ɗauka ba sa isa.

A wannan maƙala, za mu yi nazari ne kan abubuwan da za a koya daga ambaliyar ruwa, ta yadda ko da ba su magance matsalar ba gaba ɗaya ba, to aƙalla su taimaka wajen rage tsananin tasirinta.

Sai dai kafin nan, bari mu duba manyan sanadin da ke jawo ambaliyar ruwa.

Mamakon ruwan sama: Sauyin yanayi da ke jawo mamakon ruwan sama na daga cikin manyan dalilan da ke jawo ambaliyar ruwa a wurare da dama, ta yadda ruwa kan rushe, ko ya shafe gidaje da gonaki da sauran ababen more rayuwa.

Rashin isassun magudanai: A wasu yankunan kuma musamman irin na Afirka akwai matsalar rashin magudanan ruwa, saboda idan ruwa ya zo bai samu hanya ba to sai ya zama ambaliya.

Farfesa Adamu ya ce ya kuma kamata a dinga duba ƙarfin madatsun ruwa akai-akai. Hoto: Getty

Ballewa ko tumbatsar madatsun ruwa: Wannan matsala gagaruma ce da ke jawo mummunar ambaliya. A lokutan damina, madatsun ruwa kan cika maƙil ta yadda har sai an saki ruwan da ke ciki don ya ragu, idan ba haka ba kuma su ɓalle da kansu ruwan ya malale da ƙarfinsa.

Mun ga yadda a watan Satumban 2023, wasu madatsun ruwa biyu suka ɓalle a Libiya inda kubik mita miliyan 30 na ruwa ya malale ya shafe yankuna da dama a birnin Derna mai mutum 100,000, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 4,300.

Farfesa Yusuf Adamu na Sashen Nazarin Ƙasa a Jami’ar Bayero ta Kano, ya ce abu na farko da za a fahimta shi ne irin yadda wadannan masifu kamar ambaliya da girgizar ƙasa da guguwa mai ƙarfi da sauran su kan faru ne a wurare da lokuta daban-daban, amma idan suka tashi faruwa ana iya samun masaniyar za su faru, sai dai ba za a iya hana faruwarsu ba.

Masanin kuma ƙwararre a fannin bala’o’i irin waɗannan ya ce akwai darussa uku da ya kamata hukumomi da al’umma su koya, waɗanda ba a koya a shekarun baya ba.

Darasi na farko

Farfesa ya ce tun da hukumar kula da hasashen yanayi na Nijeriya Nimet kan yi hasashen yawan ruwan da za a samu ko ambaliya, to ya kamata da zarar an yi hasashen a fara shiri ba kawai gwamnati da al’umma su watsar da bayanan su ci gaba da al’amuran gabansu ba.

Ambaliyar Maiduguri ta shafi dubban mutane da jawo asarar rayuka. Hoto: Yerwa News

"A dinga tsara yin abin da ya dace don kwashe mutane daga wajen da aka ba da gargadi, musamman ta hanyar hada kai tsakanin masu hasashe da hukumomi da ma su jama’a.

"Kuma ya kasance an ba da rahoton hasashe da wuri don aiwatar da kwashe mutane a kan lokaci daga wuraren da bala’in ka iya shafa.

Darasi na biyu

Farfesa Adamu ya ce ya kuma kamata a dinga duba ƙarfin madatsun ruwa akai-akai duk bayan ‘yan shekaru don a ga me ya kamata a gyara.

"Shi dam gina shi ake yi don haka ƙarfin ruwan da ke tahowa daga cikinsa akai-akai kan raunana gini da turakunsa, ta yadda a lokaci guda idan ya gaji kuma ruwa ya masa yawa to zai ɓalle da kansa ya nemi hanyar fita.”

Ya ƙara da cewa kuma ya kamata a dinga bude madatsun ruwa lokaci zuwa lokaci don rage ruwan da ke cikinsa kuma a samar da wajen da zai tafi kai tsaye, tun kafin ya ɓalle da kansa ya yi inda ba a so.

Darasi na uku

Masanin ya ce ya kamata mutane da ke cikin garuruwa da hukumomi su fahimci cewa ba a tare wa ruwa hanya, don in dai ruwa ya taho dole sai ya nemi hanya.

“Hukumomi su samar da manyan hanyoyin da ruwa zai wuce idan ya zo da yawa. Mutane su daina toshe hanyoyin ruwa ta hanyar zuba shara a ciki ba tare da kwashewa ba. Dole kowa ya yi wa kansa fada don guje wa hakan,” Farfesa Adamu ya gaya wa TRT Afrika.

Darasi na huɗu

Farfesa ya ce akwai wasu wuraren da ke taimaka wa wajen rage kaifin ambaliya kamar koguna da kududdufai.

“Misali yanzu a Kano duk an ciccike kududdufai ana gini a kai. Don haka idan ruwan ya zo ina za shi? Dole ya kamata a dinga samar da irin wadannan wurare kuma a tabbatar an kiyaye su don kar a cika su da shara ko yin gini a kai.

TRT Afrika