Daga Abdulwasiu Hassan
Kalmomi na ban sha'awa na taken ƙasa ba wai ana rera su ne kawai ba domin saka kishin ƙasa a zukatan 'yan ƙasa. Ga 'yan ƙasa masu rera taken, yana da matuƙar muhimmanci, inda ke tunawa masu rerawar tarihin ƙasar da al'adu da burin 'yan ƙasar.
A Nijeriya, ana ta tafka muhawara kan batun hannu da Shugaba Bola Tinubu ya saka kan dokar da 'yan majalisa suka amince da ita wadda ta amince a dawo da tsohon taken Nijeriya wanda aka maye gurbinsa a 1978.
Mutane da dama sun sha mamaki kan yadda 'yan majalisar tarayya suka yi gaggawar yin dokar da amincewa da ita a cikin mako guda, inda da haka nan kawai ne za a iya ɗaukar watanni kafin a yi hakan.
Taken Nijeriya na asali wato Nigeria, We Hail Thee, an rubuta shi ne a 1960 wanda 'yar Birtaniyar nan Lillian Jean Williams ta rubuta kuma aka fara amfani da shi bayan samun 'yanci kai.
A 1978, gwamnatin Janar Olusegun Obasanjo ta maye gurbinta da Arise, O' Compatriots, wadda wani rukunin 'yan Nijeriya suka rubuta.
Bayan amincewa da ƙudirin dokar a ranar 29 ga watan Mayu, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tsohuwar wakar ta nuna kyawon bambance-bambancen da Nijeriya suke da su.
Ga tsararraki na ’yan Najeriya da aka haifa bayan 1978 kuma ba tare da tunawa da asalin waƙar ba, sake dawo da ita ya tayar da hankali.
Ra'ayoyi mabambanta
"Na fahimci akwai mabanbanta ra'ayoyi kan komawa ga tsohon taken Nijeriya. Ga waɗanda suke rera ta a wurin taron ɗalibai na safe a makarantu, akwai sha'awar sake duba Nigeria, We Hail Thee," in ji Dakta Aliyu Tilde, wanda masani ne kan harkar ilimi a tattaunawarsa da TRT Afrika.
Amma Baba Yusuf, wanda mai sharhi ne kan tsare-tsare, na ganin cewa sake dawo da tsohon taken Nijeriya, misali ne na rashin bayar da fifiko.
"Ban ga wani dalili da zai sa mu koma ga tsohon take wanda zai rinƙa tuna mana da mulkin mallaka ba," in ji shi.
"A gaskiya, na fi son Arise, O' Compatriots a matsayin taken Nijeriya fiye da Nigeria, We Hail Thee kan dalilin cewa tsohon taken 'yan Nijeriya ne suka rubuta shi kuma ga 'yan Nijeriya. Haka kuma shi sabon ya fi amfani ga burin 'yan Nijeriya fiye da sabon da aka dawo da shi."
Shin wannan rabuwar kai ce da ta samo asali daga tun kaka da kakanni wadda ba ta da alaƙa da taken Nijeriya?
Ibrahim Sheme, wanda ɗan jarida ne kuma marubuci ne ya yi tsayuwar gwamin jaki ne kan lamuran biyu. Yana makarantar firamare bayan samun 'yancin kan Nijeriya wanda a lokacin ne aka yi watsi da taken Nijeriya na farko a shekarar 1978 ba tare da ya samu dama shi da sa'o'insa sun koyi taken ba.
"Saboda sha'awa, na yi ƙoƙari na koyi ainihin taken kafin a dawo da shi kwanan nan. Lokacin da aka fara ce-ce-ku-ce, na yi mamakin ganin wani sashe na mutane suna daukar wannan batu a matsayin maras muhimmanci, suna cewa kamata ya yi mu damu da tattalin arziki maimakon haka," in ji shi.
Tsayawa a tsakiya
Sheme na ganin yadda mutane suka yi watsi da batun sabon taken hakan na hana jama'a fitowa su tattauna abubuwan da ke damunsu.
“Ba wai rashin bayar da fifiko ba ne, kamar yadda wasu ke tunani, za ka ga cewa ‘yan Nijeriya yanzu suna magana, watakila a karon farko cikin shekaru da dama, game da kasa da kishin kasa," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
"Yana da kyau kan cewa mutane na magana kan wani abu da zai ciyar da ƙasarmu gaba, gami da bukatar sake sadaukar da kanmu kan manufar Nijeriya."
A daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan ko a ci gaba da amfani da tsohon taken Nijeriya, ɗaya daga cikin damuwar da aka nuna ita ce yaran da suka kammala sakandare zai yi wuya su iya sabon taken ƙasar, wato Nigeria, We Hail Thee, da kuma ɗaukarsa a matsayin takensu.
Ɗaya daga cikin abubuwan da wannan batun ke magana shi ne duk da cewa waɗanda za su shiga jami'a da sojoji da masu wasanni duka za su koyi sabon taken a wuraren horonsu, koyon zai yi wa wasu wahala.
Sheme ya ce daukar matakin koyon taken da aka dawo da shi a matsayin wani cikas na ƙara zama matsala. "Duk wanda ya sanya hankalinsa wajen koyon wannan taken to zai iya yin hakan cikin gaggawa, gwargwadon sha'awarsa da jajircewarsa a kantsa."
Ga sabon taken na Nijeriya
Nigeria, we hail thee,
Our own dear native land,
Though tribe and tongue may differ,
In brotherhood, we stand,
Nigerians all, and proud to serve
Our sovereign Motherland.
Our flag shall be a symbol
That truth and justice reign,
In peace or battle honour’d,
And this we count as gain,
To hand on to our children
A banner without stain.
O God of all creation,
Grant this our one request,
Help us to build a nation
Where no man is oppressed,
And so with peace and plenty
Nigeria may be blessed