NAM

Daga Dayo Yussuf

Titunan Kampala sun kasance cikin jiran tsammani, yayin da wakilai 4,000 daga kasashe sama da 120 suka hallara a babban birnin Uganda, abin da mutane da yawa ke ganin wani muhimmin lokaci ne ga kungiyar 'yan ba-ruwanmu (NAM).

An kafa kungiyar ta Non-Aligned Movement a shekarar 1961 a matsayin wata kariya ga kasashe masu tasowa sakamakon yakin cacar baka da ake yi, kungiyar ta ci gaba da tafiya sama da shekara 60 ba tare da sauya muradun kafa ta ba.

Sai dai a yayin da aka fara wannan taron karo na 19 a birnin Kampala na Uganda domin tattaunawa kan makomar kungiyar, ana kara matsa mata lama kan ta yi abin da aka kafata ba a kai ba - ma'ana daukar bangare.

Duk da haka, yayin da NAM ba ta hada kai ko nuna adawa da kowace ƙungiya mai ƙarfi ba, shin ko akwai wanda zai iya fitowa karara ya ce duka mambobin kungiyar ba su "dauki bangare ba"?

Masana harkokin diflomasiyya na ganin cewa akwai kasashe mambobi da dama wadanda suka saka kansu cikin wata siyasa.

"Abu ne mai wuya kasashe su ce ba su hada kai da wata kungiya ba saboda muna zaune a wata duniya wadda muka dogara da juna," kamar yadda Dakta Edgar Githua ya bayyana, wanda malami ne kan harkokin diflomasiyya da kuma sharhi kan tsaro a Kenya a yayin tattaunawarsa da TRT Afrika.

"Mun kai wani mataki wanda mutane ba su son samun abokan gaba na dindindin. Muna son abin da ranmu ke so ne kawai, wanda hakan ke nufin mutanen da suka kasance abokai a yau za su iya zama abokan gaba gobe, wanda hakan ya dogara ne da abin da ake so," in ji Dakta Githua.

Bayan Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar ƴan ba-ruwanmu ita ce ta biyu mafi girma idan ana la'akari da yawan kasashe. NAM a halin yanzu tana da kasashe 53 daga Afirka sai 39 daga Asia sai 26 daga yankin Latin Amurka da Caribbean sai biyu daga Turai.

Haka kuma ta hada da kasar Palestine wadda ba ta cikin Majalisar Dinkin Duniya, da kasashe 17 masu sa ido da kuma kungiyoyi masu sa ido 10.

Sai dai ba kamar sauran kungiyoyin yankuna ba da na kasa da kasa, ba ta da wata doka da ta kafa ta ko wata yarjejeniya ko wata sakateriya ta dindindin.

Afirka ta Kudu ta kai Isra'ila Kotun Hukunta Manyan Laifuka ICC kan zargin laifukan yaki kan Falasidnu. / Hoto: Fadar Shugaban Afirka ta Kudu

Kasa mamba da ke rike da kujerar shugabancin kungiyar NAM ita ce ke da alhakin daidaitawa da gudanar da al'amuran kungiyar. An nada Uganda a kujerar shugabancin na tsawon shekaru uku.

Idan kungiyar ba ta da wata yarjejeniya da aka kafa ta a kai a kan baya ga akidar kungiyar da aka amince da ita ta “ba-ruwanmu”, me ya sa za a shiga cikin irin wannan yunkuri?

"Kamar yadda martanin duniya game da yakin Rasha da Ukraine, rikicin Isra'ila da Falasdinu, ko rikicin China da Amurka ya nuna, kasashe na bin lamura a hankali. Domin suna son yin aiki da kowa da kowa," kamar yadda Dakta Githua ya bayyan.

"Kasashen na NAM sun gano cewa za su iya yin rashi idan suka dauki bangare."

Tafiya mai sarkakiya

Masana sun yi imanin cewa gaba ɗaya ƙasashe suna tafiya ta hanya iri ɗaya, dangane da manufofinsu guda ɗaya. Amma ba yana nufin za a dora maka laifi ba don ka zabi kin daukar bangare.

Sakamakon haka ne, har su mambobin Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya suna da damar su ki yin zabe kan wani kudiri wanda ba su son saka bakinsu a ciki.

"Kasashe da dama sun zabi kin daukar bangare dangane da wannan inda suke mayar da hankali kan abin da zai zo nan gaba wanda Gabas ta Tsakiya ko kasashen Larabawa za su iya yi. Sai dai ba kamar Afirka ta Kudu ba wadanda suka dauki bangare, amma kusan duka kasashe na ba su son daukar bangare," in ji Dakta Githua.

Kamar yadda abubuwan da suka faru a baya suka tabbatar, an ci zarafin wasu kasashe ta fuskar siyasa da tattalin arziki saboda daukar bangaranci ba tare da zabi ko tilastawa ba.

Don haka, mene ne ya sa halin da ake ciki a duniya ya bambanta da cewa membobin NAM dole ne su sake duba cikin mawuyacin hali na kasancewa tsaka tsaki ko daukar bangare?

Kungiyar 'yan ba-ruwanmu na son ci gaba da zama wadda ba ta daukar bangare. / Hoto: Ma'aikatar Harkokin Wajen Uganda

"A siyasar duniya, manyan kasashe suna son ganin inda kuka karkata. Rasha, China, Amurka da Tarayyar Turai suna jin bukatar sanin matsayar wasu kasashe kan batutuwa na musamman saboda duniya a halin yanzu ta zama mai gasa sosai," kamar yadda Dakta Githua ya bayyana wa TRT Afrika.

Mu ko kuma su

Tsoron daukar matakin da bai dace ba kan kowane lamari, musamman idan abin da zai haifar ya yi nisa, na iya sanya kasashen su shiga rukunin wadanda ba lallai ba ne su yi ra'ayi daya da su.

"Daya daga cikin manyan manufofin kungiyar NAM shi ne ci gaban ajandar cewa idan ba na son goyon bayanku, ko za ku iya kyale ni?" in ji Dakta Githua/

"Wannan shine sabon tunani a can. Ka bar mu; Kada ku ja mu cikin fadanku. Wannan zabin shi ne abin da kasashe mambobin ke kokarin karewa. Idan aka yi la’akari da inda duniya ta dosa, ana matsa wa kowa da kowa ya ɗauki matsayi a kan kusan komai."

A taron kungiyar ta NAM karo na 19, batutuwan da suka fi daukar hankali sun hada da yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, ikon mallakar kasashe mambobin kungiyar, rikicin Somaliya da Habasha da ke kara ta'azzara, rikice-rikicen makamai a sassa daban-daban na duniya, karancin abinci, hijira, rashin aikin yi, annoba, canjin yanayi, da ta'addanci.

Wakilan za su kafa kwamitoci guda biyu - na siyasa da na tattalin arziki - wadanda takaitaccen bayaninsu shi ne hada wata tattaunawar da za ta tsara daftarin na musamman a Kampala. Ministocin harkokin wajen kasashen ne za su amince da hakan, sannan su bayyana a taron shugabannin kasashe.

Dr Githua ya hango kalubale ga kungiyar don ci gaba da da kokarin daidaita lamura da kuma daukar hakan da muhimmanci.

"Wannan zai zama lamari mai sarkakiya," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika. "Yawancin wadannan kasashen NAM suna da ra'ayi mai karfi kan batutuwa da dama. Har ila yau, yawancin batutuwan suna da alaka da muradunsu. A karshe za su dauki matsaya," in ji shi.

TRT Afrika