Kamfanonin ƙera makamai ba bisa ƙa'ida ba a Nijeriya, wadanda galibi ke mayar da kasuwancinsu halattacce, na ƙara zama barazana ga tsaron cikin gida da zaman lafiyar al'ummar kasar.
Girman wannan matsala dai na nuna yadda ƴan sanda kasar suka bankado wasu jerin haramtattun masana'antun kera bindigogi a kasar wadda ke yankin yammacin Afirka.
Kamfanonin sun kwafi nau'in bindiga ƙirar AK-47 da bindigogin ganga da kananan bindigu da kuma harsashai - da dai sauransu, waɗanda suke kera su.
A watan Oktoban bara ne, masu bincike suka kutsa kai cikin wata masana'anta kera makamai a jihar Legas wadda ke kan gaba wajen kera makamai ba bisa ka’ida ba, lamarin da ke nuni da hazakar masu kera irin wadannan haramtattun kayayyaki.
"Duba da yadda aka yi amfani da kwarewa wajen kera bindigar nan ta AK-47. Ba abin mamaki ba ne," kamar yanda mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi ya bayyana a shafin X a kwanan nan.
Jami'in ya ɗora hotonsa yayin da yake nuna wasu makamai da ake zargin an ƙwato su ne daga wata masana'antar ƙera bindigogi da ke jihar Filato.
A baya-bayan nan ne sojojin Nijeriya suka kai wani samame a wata masana'anta irin wannan a jihar Delta dake kudancin kasar.
Yanayin kusan iri daya ne, daga jihar Filato da ke yankin tsakiyar Nijeriya zuwa Legas da ke kudu maso yamma.
Jami’an tsaro sun kai samame kan masana’antu, inda suka ƙwato makamai da dama tare da yin kame, sai dai ayyukan ƴan bindigar a kasar na ƙara yawa.
"Kasuwancin haramtattun makamai ya fi yawa a yankin kudu maso gabashin Nijeriya da kuma arewa ta tsakiyar kasar, " kamar yanda Kyaftin (mai ritaya) Sadiq Garba Shehu ya shaida wa TRT Afrika.
Matsalar Yammacin Afirka
Kalubalen bai tsaya ga iya Nijeriya kadai ba. Kasashe da dama da ke makwabtaka da kasar, ciki har da wadanda ke fama da rikice-rikicen cikin gida da hargitsin siyasa, suna fama da wannan matsala da ke neman kai musu wankin hula dare.
Bisa ga labarin shafin Relief web da ke wallafa bayanai karkashin ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, akwai masana'antu da ke ƙera bindigogi ba bisa ka'ida ba da suka shafe tsawon lokaci a kasashe kamar Mali da Senegal da Togo da Saliyo da Laberiya da Guinea da Mali da Benin da Burkina Faso da kuma Ivory Coast.
Wani rahoto na shekarar 2018 kan ayyukan kafafen yanar gizo a tsarin zaman lafiya da tsaro na kungiyar ECOWAS ya zargi kamfanoni masu kera bindigogi ba bisa ƙa'ida ba a kasar da aka bar mallaka da kuma yaduwar makamai a hannun fararen hula”.
Baya ga rarraba kananan bindigogi, ana alakanta wannan lamari da kara tabarbarewar rikice-rikicen cikin gida a kusan dukkanin kasashen da abin ya shafa, musamman a yankunan Yammacin Afirka.
Kungiyar ECOWAS dai ta sha yin kira ga kasashe mambobin kungiyar da su dauki tsauraran matakai domin dakile yaduwar haramtattun makamai a yankin.
Yayin da gwamnatoci da dama suke kan iya kokarinsu wajen kawo karshen ayyukan kera bindigogi, ana iya cewa ba wai kawai haramtattun kamfanonin kera makaman sun samu wurin zama ba ne, a kasashe da dama ciki har da Nijeriya, ga dukkan alamu masana'antun na kara bunkasa karkashin hancin hukumomin tsaro.
Hanyoyin gudanar da ayyukansu
Haramtattun kamfanonin a Nijeriya sun yi kaurin suna wajen samar da nau'in kwafin makamai waɗanda da wuya a iya bambanta su daga na asalin.
“Duk wadannan bindigu an yi su ne a cikin (haramtacciyar) masana’antar a Jos. Mutanen suna da hazaka,” a cewar mai magana da yawun ‘yan sandan kasar Adejobi, inda ya saka hoton bindigu guda tara da aka kwato a shafinsa na X.
To, me ke karfafa ayyukan haramtattun masana’antun kera bindigogi a yankin?
"Aikata laifuffuka na kara rura wutar bukata," in ji Kyaftin Shehu. " Rikicin kabilanci da na addini ya haifar da ƴan bindigar kabilanci, wadanda a zahiri ba su iya samun makamai ta hanyar doka."
A cewar manazarta, bindigogin da aka kera daga cikin wadannan haramtattun masana'antu suna dauke da adadi masu yawa daga cikin wadanda ke yawo.
Kyaftin Shehu ya ce haramtattun masana'antun "sun taimaka da kashi 40 cikin dari na matsalar".
Canja dabarun
Martanin sakon da Adejobi ya wallafa a shafinsa na intanet ya yi nuni da cewa ƴan Nijeriya da dama suna ganin ya kamata hukumomin tsaro su tunkari matsalar ta wata hanya daban.
“Muna bukatar yin aiki da su, domin amfanin mu,” kamar yadda kakakin ƴan sandan ya rubuta, inda ya ja hankali kan tsokacin da ya bukaci hukumomi su yi amfani da “hazukai” daga wadanda ke kera makamai ba bisa ka’ida ba domin amfanin kasa.
Kyaftin Shehu ya bayyana cewa furta hakan ya fi saukin aiwatarwa. "Ba shi yiwuwa a yaye su daga kera bindigogi ba bisa ka'ida ba tun da mafi yawan lokuta sukan kafa hujjojinsu kan neman kudi ko kuma ra'ayi na addini," in ji shi.
Ko ma wace shawara aka dauka, muradin gwamnati da al’ummar wannan yanki shi ne samun tsaro kuma burinsu shi ne a rage barazanar yaduwar makamai da masana'antu ke kera su ba bisa ka'ida ba kuma batare da lasisi ba.