Daga Charles Mgbolu
Wani batu da babu kuskure a ciki game da wasannin Olympics na zamanin yau shi ne yadda ake da bakaken fata da yawa a tarihi, ba tare da duba da kasashen da suka fito da irin wasannin da suke yi ba.
A ranar 26 ga Juli za a fara sabuwar gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympics a Paris, lokaci ne na Afirka ta sake haskawa - a wannan karon, fiye da yadda aka saba gani.
Gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympics ta 2024 za ta kasance mai haskaka wadanda ke halartar wasannin a karon farko.
A wannan karon, za a yi wasannin a Faranss abayan shekaru 100, kuma 'yan wasa 10,500 ne za su fafata don lashe kambi 329 a wasanni 32 kuma cikin kwanaki 19.
A karon farko za a gudanar da faretin gasar a wajen filin wasannin tsalle-tsallen, kuma ana sa ran tawagogi za su tafi da jiragen ruwa zuwa Seine.
Gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympics ta Paris 2024 ce za ta zama ta farko da ake da adadi kai daya na yawan 'yan wasa mata da maza.
Wasa na farko da ke halartar gasar da ya fi jan hankalin kafafan yada labarai tun bayar da sanarwar gasar a 2020 shi ne wani salon rawar birane daga New York, wanda za a yi a matsayin wasa a wajen.
Babban fili, kambi da yawa
Masu horarwa da masu sharhi kan harkokin wasanni sun gamsu cewa kambin da Afirka ke sabu gaba daya na iya daduwa tare da shiga wasanni da yawa, musamman ma wasannin gargajiya.
Kenya, kasar Afirka mafi samun maki, ta lashe kambi 10 a gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympic da ta gabata da aka gudanar a Tokyo, amma kuma 'yan wasan Amurka sun lashe kambi 113.
Wannan ne lokacin da ya kamata mu zauna mu yi tunani a matsayin mu na Afirka tare da tambayar "Me ya sa ba za mu karfafi damar da muke da ita ba a gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympics don ganin an saka wasannin gargajiya na Afirka a jerin wasannin?" in ji mai horar da wasan ninkaya Christopher Ezemegwalu, yayin da yake tattauna wa da TRT Afirka.
Mai bayar da horo kuma kwararre dan Nijeriya Balogun Olanrewaju ma na da irin wannan ra'ayi.
"A koyaushe Afirka na gabatar da 'yan wasa da yawa a gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympic, amma kuma hakan na dace wa da mu ne ta yadda ake fahimtar mu 'yan Afirka ne a gasar, ba wai kawai a matsayin masu lashe kambi d ayawa ba, har ma da zama wadanda suka kirkikri wasu wasannin." in ji shi.
Gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympic ta 2020 da aka yi a Tokyo ta gabatar da sabbin wasanni da suka fito dga kasashe daban-daban: karate daga kasar China, hawa takalmi mai taya daga Amurka, wasan hawa gini daga Faransa da wasan Hawaii.
Gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympic a Los Angeles a 2028 zai gabatar da baseball daga Arewacin Amurka, T20 cricket daga Birtaniya, kwallon kafar tuta daga Amurka, lacrosse daga Amurka, da wasan kwallon squash daga Birtaniya.
Matattarar wasannin gargajiya
Afirka mahaifar wasannin gargajiya da dama da suka samu karbuwa a duniya.
Dambe, tsohon wasa ne na gwada kwarfi da hausawa ke yi a arewacin Nijeriya. 'Dambe Warriors', wata tashar YouTube na da mabiya sama da 196,000, bidiyo 801, da kuma yawan kallo miliyan biyu.
Wani misalin shi ne wasan Laamb na Sanagal, shi ma wani nau'in wasan kokawa da aka nuna a wani fim da 'yan Amurka da Ingila suka fito a matsayin jarumai a 2008.
A Kenya, Wasannin tsalle-tsalle na Maasai sun mayar da wasannin gargajiya zuwa cikakkun wasannin zamani, kamar su Tsallen Adumu Maasai, wand ayanzu ya zama wasa a hukumance, da rungu, wanda irin wasan javelin ne.
Olanrewaju ya bayar da shawarar habaka wa da tallata wasannin gargajiya na Afirka a duniya kafin su fara gangamin neman a saka su a gasar wasannin tsalle-tsalle Oylmpic.
"Ba za mu samu nasarar wasanninmu na gargajiya ba matukar ba mu tsaya mun tsara su ba, mu samar da tsayayyun dokoki, sannan mu yada su a dukkan nahiyar Afirka," in ji Olanrewaju ga TRT Afirka.
Shirin Wasanni na IOC ya kara fito da wannan damuwa, a cikin kundin bayansu sun bayyana cewa dole ne duk wani wasa da ke son a saka shi a jerin wasannin gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympics idan na maza ne ya zama ya samu karbuwa a kalla a kasashe 75 kuma a nahiyoyi hudu, sannan idan na mata ne a kasashe 40 kuma a nahiyoyi uku.
IOC sun kara da cewa dole ne wasannin da ake son saka su a gasar su zama sun cika sharuddan kasa da kasa ta fuskar yawa da kasashen da ake yin su, sannan dole ne su zama an yi su a kalla sau biyu a gasar nahiyoyi.
Dabarun habaka wasanni a cikin gida
"Idan ba mu habaka da tallata wasanninmu na gargajiya a tsakaninmu ba, a matsayin mu na 'yan kasashen Afirka, ta yaya za mu tallata su ga duniya? in ji Olanrewaju cikin mamaki.
"Dole ne mu kasance masu wasannin kawo cigaba ta hanyar kaddamar da wadannan wasanni a makarantun firamare da sakandire, d akuma kai wasannin sauran kasashen Afirka, idan har da gaske muke yi game da bukatar saka wasannin Afirka a gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympic."
Babban mai horarwa Ezemegwalu ya lura da cewa dole Afirka ta shirya wajen zuba jari d amanufar habaka wadannan wasanni su samu karbuwa a cikin gida da maye gurbin wasannin tsalle-tsalle na Turai, idan har ana son IOC su karbe su.
Ya ce "Dole ne a matsayin mu na nahiya mu dauki kasuwancin wasanni da muhimmanci. Za mu rasa damar idan har ba mu habaka wadannan wasanni a kasashen Afirka ba, kuma idan ba haka ba kasshen Turai za su iya dauke wasannin, su baiwa 'yan wasa horo su ji gajiyarsu."
Dan jaridar wasanni na Ghana Victor Adjei ya yi amanna da cewa da zarar an cika sharuddan da ake bukata, cikin sauki za a samu nasarar amincewa da wasannin gargajiya na Afirka. "Nau'ikan ninkaya, sun taba zama wasannin gargajiya a kasashe daban-daban."
Morris Momo, shugaban kulob din ninkaya na Liberia, ya ce dole ne Afirka su yi aiki wajen kara yawan wasanninta da za a yi su a gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympic, wanda hakan zai kara yawan kambin da nahiyar ke samu.
Ya ce "Muna da basirar gudu a kan ruwan teku a nan Liberia. Muna da wuraren wanka a gabar teku da dama. Amma ba ma tunanin Olympic a yanzu saboda ba mu da allunan wasannin ko kwararru da za su ba wa mutanenmu horo. Dole ne mu raini matasa maje gaba da za su wakilci kasashenmu da nahiyar."
Ezemegwalu ya bayar da shawarar kwakwaiyar tsarin Turai na aiki daga tushe. Ya fada wa TRT Afirka cewa "Muna bukatar kafa cibiyoyin habaka wasanni a kowanne yanki. Wannan abu ne da ya shafi raina da karfafa gwiwar matasa."
A yayin da ake rura wutar fara gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympic a Paris, Afika na da manufar dawo da karsashin burinta na gina abinda ake da shi - basira, al'ada da karfin zuciyar yin nasara.