Daga Firmain Eric Mbadinga
Daga cikin abubuwa masu ban ta'ajibi a hallittun tsirrai, shi ne wata bishiyar fure da aka bai wa sunan "Zuciya mai zubar da jini," wadda ake amfani da kyawunta wajen bayyana yanayin halayyar ɗan'adam da ba a bukata.
A yayin da wannan bishiya ba ta zubar da jini a zahiri, hotuna da bidiyo a fadin duniya na nuna yadda wasu bishiyoyi suke fitar da wani jan ruwa kamar jini, abun da ke ci gaba da tayar da hazo kan fassararsa a gargajiyance da kimiyyance a tsakanin al'ummu.
A yankuna irin su Kudancin Amurka, ana kuskuren kallon wannan ruwa a matsayin jini, yayin da a Afirka, abin da aka fi imani da shi shi ne wai wasu mutanen boye ne da ke rayuwa a cikin bishiyoyin ke fitar da jan ruwan.
A watan Oktoban 2017, masanin tsirrai dan kasar Faransa ya bayar da haske kan yadda Tepezcohuite ko "bishiya mai aman jini", ta zama abar girmamawa a wajen jama'ar Mayas da ke kudanci Mexico zuwa Guatemala.
Wani bidiyo da aka yada a yanar gizo ya tabbatar da wanzuwar irin wadannan bishiyoyi masu zubar da ruwa kamar jini. Mene ne abin da ake muhawara a kai game da wannan jan ruwa da ke bulbulowa?
Ya samo asali daga al'adu
Kimiyya ta yi watsi da wannan abi bisa cewa camfi ne kawai idan aka ce wai wannan ruwa d abishiyun ke fitarwa jini ne. Amma jama'ar Shaman da masu bin addinan gargajiya na yi wa wadannan bishiyu kallon masu tsarki.
Dr Djibril Diop, masanin muhalli kuma malami a Jami'ar Cheikh Anta Diop da ke Dakar babban birnin Senegal, ya bayyana cewa babu wata bishiya da ke aman jini ko take da wani ikon amfanarwa ko cutarwa saboda jan ruwan da take da fitarwa.
Ya nanata cewa wannan ruwa wani danko ne ko ruwan cikin tsirrai danda ke taka muhimmiyar rawa wajen rayuwarsu.
Dankon cikin tsirrai wani ruwa ne da ke fita daga bishiya don tsaron kanta, inda ruwan cikin jijiyoyin bishiya kuma yake kasancewa fari, kuma yana fita da tsakanin gajye da reshe, wanda shi ke kai ruwa, gishiri, ko sukari ga tsirrai.
Dr Diop ya bayar da misali da bishiyar darbejiya a yankin Bandafassi take fitar da wani farin ruwa mai yawa saboda harin ciwon fungal.
Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Mazauna yankin na fassara wannan da wani abin ta'ajibi kan bishiyar, ba tare da sun san cewa yanayin bishiyar, yankin da take, kasar d ata fito daga ciki da kuma yanayin ciwon da za ta yi na taka rawa wajen fitar ruwan da kalarsa.
Masanin muhallin ya kuma yi nuni da cewa babu wata bishiya da ke da jini, a saboda haka a hankalce, ba za a taba tsammanin ta fitar da jini ba.
Ya bayar da misali da bishiyar da ake kira Socotra don nuni ga yadda danko a ruean bishiya yake, tare da kalar jan da wasu ke tunanin ko jini ne.
Wannan bishiya da za ta iya tsayin har mita 20, na fitar da ruwa ja d aya sanya har aka rubuta wasu makalolin kimiyya don bayyana ta a matsayin "bishiya mai aman jini".
Wannan jan ruwa ya hada da sukari, ruwa da wasu sinadaran gina jiki, kuma a wasu al'adu ana amfani da shi wajen rini. Ana yawan alakanta wannan ruwa ja ga karfin tace sinadarai da bishiya ke yi.
Darajar yin magani
Baya ga amfani da su wajen yin rini, masana tsirrai irin su Dr Diop da masu maganin gargajiya irin su Romaric Moussounde Moussounda na da ra'ayin cewa wadannan bishiyoyi na yin magani.
Moussounda, wanda ke da fahimta kan bambance-bambancen dazukan Gabon, na da ra'ayin cewa halittu da yawa, ko nau'ikan bishiyoyi Pterocarpusda ke Afirka ko na Abitibi da ke Quebec, duk sun cancanci a yi musu kallon masu matsayi na musamman ko yin camfi game da su.
Moussounda ya fada wa TRT Afirka cewa "Wadannan bishiyoyi kyauta ce daga Ubangiji da bai kamata su fada wani rukunin rashin tabbas ba."
"Wannan ruwa da ke fitoa daga cikin wadannan bishiyoyi na jini ba ne, amma kuma na da muhimmanci da matsayi irin na jini."
Moussounda wanda ke cakuda gargajiyanci da zamananci a fannin kula da lafiyar zuciya da sauran ayyukan gaggawa na kula da lafiya, ya rawaito marubuci dan asalin Senegal Birago Diop, wanda a 1960 ya yi rubutu game da "Tsarkin wasu bishiyoyi".
Moussounda ya ce "Ana yawan amfani da wadannan bishiyu masu tsarki wajen bukukuwa da magani. Duk suna da wata alaka ruhaniyya ga dan adam."
A yayin da masana tsirrai ke ta fashin baki kan wadannan bishiyu masu aman jini, su kuma mabiya addinan gargajiya irin su Mayan da ke Mexico da 'yan asalin Indiya na Barazil ko Kudancin Amurka na da ra'ayin lallai a kalli wadannan bishiyoyi a matsayin masu tsarki ababan girmamawa.
Duk da wadannan bambance-bambance na ra'ayi, akwai ijma'i tsakanin masana kan lallai a kare wadanna bishiyoyi, ko suna da tsarki ko babu, don kare muhalli.