Kocin dan Nijeriya ya rasa kafarsa ta hagu sakamakon hatsarin mota wanda ya rutsa da shi, lamarin da ya kawo karshen mafarkinsa na taka leda. / Hoto: TRT Afrika

Auwal Khamis Umar wanda aka fi sani da AK Nasara, yana aiki kamar duk wani ƙwararren kocin ƙwallo - mutum ne mai tsari game da wasan, mai iko a cikin tsare-tsarensa, da rashin karɓar uzuri a rayuwa, kamar yadda yake a wasanni, ya rayu da wannan falsafar.

A lokacin da dan Nijeriyar ya rasa ƙafarsa ta hagu sakamakon hatsarin mota, yana ta tunanin yadda zai cimma burinsa na rayuwa, amma bai yarda ya yi watsi da wannan mafarkin nasa ba.

Makonni bayan an sallamo shi daga asibiti bayan an yanke kafarsa, sai tsohon dan wasan wanda a yanzu yake da shekara 43 ya koma aikin koci. Shawara ce wadda ta sauya rayuwar Umar.

"Na fara ne da horas da yara da wadanda muke buga ƙwallon kan layi kafin aka yanke kafata. Ba abu ne mai sauƙi ba, musamman ga 'yan kungiyarmu na baya. Sai na tashi daga wanda yake wasa tare da su zuwa wani wanda ya yi musu kutse da yankakar kafa," kamar yadda Umar ya shaida wa TRT Afrika.

Umar ya bayyana cewa a wani lokaci wasu 'yan wasa kan yi masa rashin kunya inda suke kalubalantar hukuncinsa na koci.

"Idan na yi wani yunkuri na sauya dan wasa sakamakon rashin kwazonsa, ina fuskantar turjiya. Sai dai na ci gaba da dagewa har suka mika wuya," kamar yadda ya bayyana.

'Yan wasan kwallon kafa sun yi zarra a gasanni daban-daban inda suka samu kulob-kulob a Turai. / Hoto: TRT Afrika

Sai dai a yanzu, "kocin mai kafa aya" yana zuwa wurare, inda sunansa na Nasara ya kasance linzami a gare shi.

Mafari mai kyau

Kamar sauran sassan duniya, ƙwallon kan titi na daga cikin rayuwar 'yan Nijeriya. Filin ƙwallon zai iya kasanewa wani budadden wuri a kan titi, ko wani fili wanda ba a amfani da dashi ba ko wata gona.

Umar ya koyi kwallon kafa a wani dan karamin fili a birnin Jos na Jihar Filato. Yayin da yake kara girma, haka soyayyarsa da kwallon kafa ke karuwa. Ya bar wasan kwallon kafa na titi domin kafa wata kungiyar kwallon kafa ta cikin unguwa.

Umar ya koyi buga kwallon kafa a lokacin da yake girma a birnin Jos. / Hoto: TRT Afrika

An soma gano irin baiwar da yake da ita ne a daidai lokacin da ya hadu da wannan kaddarar, wanda hakan ya kawo karshen mafarkin nasa.

A matsayinsa na koci, cikin lokaci kadan Umar ya fahimci cewa akwai bukatar ya kara sabunta iliminsa na kwallo.

"Na soma halartar wurin horas da 'yan wasa na manyan kungiyoyin wasanni na cikin unguwa domin koyo daga kwararru. Wannan ya taimake ni ta hanyoyi da dama," kamar yadda ya tuna.

Samun dama

Umar ya samu dama bayan kusan shekara daya bayan wani karamin kulob, Dutse Uku United ya dauke shi domin ceto shi daga wargajewa. Kalubalen ya kasance mai wuya kamar yadda zai iya samu, kuma da farko ya bukaci gano yadda zai zama daidai da aikin.

"Da farko na hakura da karbar tayin,” in ji Umar, “Amma na sake yin tunani na biyu kuma na amince da aikin farfado da kulob din, wanda a lokacin yake fama da rigingimun cikin gida da kuma rashin sakamako mai kyau.

Umar ya koyi kwallon kafa a lokacin da yake tasowa a birnin Jos da ke tsakiyar Nijeriya. / TRT Afrika

Makonni na farko sun kasance masu zafi, sakamakon 'yan wasa da dama na kungiyar sun fita daga kulob din. Sai daga baya ya yanke hukuncin amfani da abin da yake da shi a kasa.

"Sai na tara 'yan wasa, wadanda akasarinsu sun tarwatse. Sai na yi kokarin karfafa musu gwiwa domin su yarda da kansu. A kasa da wata uku, sai muka soma samun sakamako mai kyau na kokarinmu. Sai sakamako mai kyau ya fara bayyana a zahiri," in ji shi.

Irin nasarar da 'yan wasan suka soma samu a karkashin horaswar Umar ya jawo hankalin mutane. Irin jinjinar da ake yi wa kulob din ya jawo wadanda suka bar kulob din a baya suka so su dawo.

"Sai na yi sauri na dakatar da su," in ji Umar, inda ya tsaya kan bakarsa ta kin komar da su cikin kungiyar.

An ci gaba da fafatawa

Duk da irin nasarar da suka samu, kocin ya ci gaba da fuskantar kalubale a aikin da yake yi, daga ciki har wariya saboda nakasarsa.

Umar ya tattara kan 'yan wasan da suka tarwatse domin farfado da kulob din. / Hoto: TRT Afrika

"Wasu daga cikin magoya baya kan kira sunana ko na iyayena domin su zage mu," kamar yadda Umar ya bayyana.

"Haka kuma a duk lokacin da fili ya yamutse da rikici wanda lamari ne da aka saba da shi a kwallon kafa, ina shan wahala wurin tsira sakamakon ba zan iya gudu ba.

Sai dai wahalar ta biya bukata ganin cewa kulob din na Umar ya samu ci gaba matuka a karkashin ikonsa.

Irin dagewar da ya nuna da jijircewa wurin farfado da kulob din ya jawo wa kungiyar lashe kofuna da yawa a Jos, irin wadanda kungiyoyi kadan ne za su iya alfahari da hakan.

TRT Afrika