Farashin dalar Amurka ya samu koma-baya a ranar Talata, a lokacin da ƴan kasuwa suke sa ido kan fitar da alƙaluman tattalin arizikin Amurka da za su ba da haske kan lokacin da Baitul Malin ƙasar zai fara rage yawan kuɗin-ruwa.
Farashin kuɗin kirifto, Bitcoin, ya yi tashin gwauron zabi irinsa na farko a cikin shekaru biyu, inda kowane ɗaya ya haura $57,000 bayan wani babban kamfanin manhaja MicroStrategy Inc ya bayyana cewa ya sayi kimanin bitcoin 3,000 a kan dala miliyan 155 miliyan.
Darajar dalar Amurka, wacce ake amfani da ita wajen auna ƙarfin sauran kuɗaɗe kamar euro da yen, ta faɗo zuwa 103.77 a kasuwar hada-hada ta Asian Time, bayan ta faɗi da kashi 0.17 a ranar Litinin.
Ƴan kasuwa sun fitar da rai cewa za a rage kuɗin-ruwa a wajen taron da za a yi a watan Maris, sannan a baya-bayan nan sun cire tsammani da suke yi na rage kuɗin-ruwa a watan watan Mayu zuwa Yuni.
Darajar dala ta faɗi da kashi 0.13 kan kowane yen 150.485, a yayin da kuɗin ƙasar Japan ya samu tagomashi bayan fitar da wasu alƙaluma da suka nuna cewa hauhuawar farashi ta tsaya a kashi biyu cikin ɗari kamar yadda bankin ƙasar ya yi hasashe.