Daga Hamza Kyeyune
Dare na maye gurbin rana, Afirka na gwagwarmaya da kalubalen jama'a matasa da kuma daduwar shekarun da aka yi hasashe za a rayu a duniya sakamakon ci-gaban kimiyya, cimaka da kula da lafiyar al'umma.
Daya daga cikin manyan kalubale shi ne tsarin kula da mutum bayan ya bar aiki, wanda ya hada da kudaden fansho da ake biyan ma'aikata bayan sun yi ritaya, kudaden na da taken "Ajiye ni yau, zan taimaka maka gobe".
Kwararru sun lura da yadda wannan bai zama wani abin damuwa ga kasashe da dama na nahiyar Afirka ba, idan aka yi duba ga wasu manyan matsaloli na bangarorin lafiya, ilimi, ayyukan noma, tsaro da sauran su.
Kungiyar 'Help Age International' ta bayyana cewa sama da kaso 60 zuwa 80 na jama'ar Afirka matasa ne.
Adadin tsofaffi ya karu da kaso 50 a tsakanin 2000 da 2015. Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa nan da 2050, za a samu karin kusan mutane biliyan biyu a duniya baki daya, wadanda kusan kaso 80 daga ciki za su fito ne daga kasashe masu tasowa.
Baraka babba da ke bukatar a magance
A yanzu Afirka na wani matakin sauyin yawaitar jama'a a tarihin nahiyar, inda tsofaffinta suke kara yawa. Duk da haka kasashe da dama ba su da tsarin fansho na kula da mutum bayan ya tsufa.
Kasa da kaso 10 na tsofaffi a Afirka ne ke cin moriyar tsarin fansho, kamar yadda wani nazari mai taken "Tsarin Fansho na Kasa da Kasa" ya nuna.
Alkaluman da wakilan taron shekara-shekara karo na hudu da aka gudanar a Kampala, babban birnin Uganda sun nuna girman wannan matsala.
Wakilan da suka halarci taron mai taken "Tsarin Fanshi Mai Dorewa a Afirka", sun bayyana cewa mutanen Afirka da ke aiki miliyan 600 daga cikin miliyan 778 ba sa kan tsarin fansho. Wannan na nufin za su fada talauci shekaru 20 bayan sun bar aiki, kuma sun yi tsufan da ba za su iya wani aiki ba.
Uganda a matsayin misali
Uganda, daya daga kasashe 15 mambobin APSA, na da mutane miliyan uku da aka yi wa rajistar fansho, wanda ba wani adadi ne mai yawa ba idan aka kalli adadin mutane miliyan 20 da ke aiki.
Martin Nsubuga, shugaban hukumar fansho ta Uganda (URBRA), ya jero manyan batutuwa da suka sa aka gaza sanya 'yan kasar Uganda a tsarin fansho da ajiyar kudade, yana mai cewa batutuwan su ne rashin aikin yi, talauci, rashin daidato a fannin samun ilimi da kasa ajiye kudade daga ma'aikata.
Mafi yawan 'yan kasar Uganda ba su da wani tsari da zai kula da rayuwarsu bayan barin aiki kamar kula da lafiya, wajen zama mai kyau da zuwan kudade a-kai-a-kai.
Mutanen da ba sa kan tsarin fansho na dogara ne kan wasu hanyoyi da iyalansu don rayuwa. Matsalar ita ce, kamar yadda yake a wasu yankunan na duniya inda ba a da masu dogaro kan wasu da yawa, matsin lambar zamantakewa za ta sanya da wahala tsofaffin Afirka su dogara kan 'yan uwa da dangi, kuma su iya rayuwa cikin jin dadi.
Kwararru sun bayar da shawarar sake duba ga tsarin dokokin da ake da su, ta yadda za a tursasa wa bangarori masu zaman kansu su saka ma'aikatansu a tsarin fansho, wanda sai gwamnatoci sun bayar da goyon baya kamar irin rage haraji ko janye shi ga masu bayar da ayyukan yi, da kuma kason gwamnati a tsarin na ritaya.
Mamba a majalisar dokokin Uganda kuma masanin tattalin arziki Muwanga Muhammad Kivumbi, wanda ke wakiltar yankin Butambala, ya yi amanna cewa kasashen Afirka da suke da tsarin fansho da ajiya don gobe, za su iya tattauna yadda za su shigar da wadanda ba sa aiki da tsarin.
"Amma ga kasashe irin su Uganda da wasu da dama inda kaso 10 kawai ne suke kan tsarin fansho, tattaunawar za ta zama ta daban," in ji shi yayin tattaunawa da TRT Afirka.
"Ba za ka iya tattauna batun kara yawan aiki da abin da babu shi ba. Muna bukatar amincewa da cewar ba mu da tsarin fansho, mu bayyana girman matsalar da ke gabanmu, sannan mu magance ta cikin gaggawa."
Bukatar sauya halayya
Lydia Mirembe, manajar sashen hulda da jama'a a URBRA ta ce babban kalubalen ma shi ne yadda za a samar da yanayin dogaro kan kudaden mutum bayan ya yi ritaya, wanda ya dogara ne kan shawarar da mutum ya yanke.
Ta ce "dokar da gwamnati ta yi ce ta kafa hukumar URBRA. Yanzu aiki ya rage ga daidaikun mutane su kalli makomarsu, su amfana da wannan dama su shirya wa ritaya tun yanzu."
"Wannan ba ya nufin wai masu bayar da ayyuka su daina sauke nauyin da ke kansu ba. Tsarin dokar da ake da shi ya ce lallai ne su dinga biyan gudunmawarsu a madadin ma'aikatansu."
Asiimwe Aine, malamar makaranta da ke aiki a karkashin gwamnati, na daga cikin miliyoyin da ke tsoron dan albashin da suke karba mara yawa zai hana su ajiye wani abu don amfanin rayuwar su bayan barin aiki.
Ta shaida wa TRT Afirka cewa "a lokacin da koma cirar kudi daga ajiya, to babu tabbas in har kudaden da za ka ci gaba da karba za su haura shekara goma."
Shekarun da aka yi hasashe bayan ritaya na rayuwa tsakanin 20 da 30 ne, ana da tsarin kula da lafiya da fasaha da suke inganta rayuwar mutum da kara tsawon ta. Asiimwe na kallon hakan a matsayin cin nasarar rabin tafiyar.
Ta ce "Ya zama wajibi gwamnati ta fara karfafa tsarin Inshorar Lafiya na Kasa, saboda zai taimaka wajen kashe kudade kadan wajen kula da lafiya."