Mutane na layi domin kada kuri'unsu a Harare babban birnin Zimbabwe./Hoto: Reuters

A karon farko bayan samun ‘yancin kanta na tsawon lokaci, Jam’iyya mai mulki ta ZANU-PF a Zimbabwe za ta shiga zabe ba tare da jerin manufofi da alkawuran zabe ba.

A maimakon haka, wannan ya kasance wata ba’a ce ga nasarorin da Shugaba Emmerson Mnangagwa, mai shekara 80, ya samu a shekaru biyar da suka gabata wanda a halin yanzu yake neman wa’adi na biyu kuma na karshe.

Gwamnatin ta bayar da misalai da ci-gaban da aka samu ta fannin ababen more rayuwa da suka hada da tituna da habaka ayyukan gona da gina madatsun ruwa wadanda aka yi su domin ban-ruwa.

Sai dai ‘yan Zimbabwe na fama da matsalolin da aka yi fama da su a lokacin zaben kasar na 2018 – tattalin arzikin da ya lalace da rashin kyawun gwamnati da kuma fuskantar wariya da takunkumi daga hukumomi da kungiyoyi masu bayar da lamuni wadanda kasashen yamma ke iko da su.

Mnangagwa, wanda aka fi sani da “the crocodile”, wato kada, ya kasance mataimakin shugaban kasa ga Robert Mugabe wanda aka hambarar a 2017.

Shekara guda bayan ya zama shugaban kasa, ya samu nasara a zaben da ke cike da takkadama.

Shugaba Emmerson Mnangagwa daga haggu sai kuma abokin takararsa Nelson Chamisa a lokacin zaben kasar na 2018. Hoto/Others

Babban abokin hamayyar Mnangagwa kusan rabin shekarunsa yake da su.

Nelson Chamisa, mai shekara 45, ya kasance mai wa’azi kuma tsohon shugaban dalibai wanda a halin yanzu yake takara a karkashin Jam’iyyar Citizens Coalition for Change wato CCC.

Nelson Chamisa ya yi alkawarin habaka tattalin arzikin kasar da kuma inganta bangaren lafiya, bangaren da ya fuskanci tserewar likitoci da dama wadanda suka gudu kasashen waje domin samun rayuwa mai kyau.

Mutum 11 ne ke fafatawa a zaben shugabancin kasar inda hukumar zaben kasar ta ce akwai mutum miliyan 6.6 da suka cancanci jefa kuri’a a kasar.

Akwai bukatar dan takara ya samu sama da kashi 50 cikin 100 na kuri’un da aka jefa kafin a sanar da shi a matsayin wanda ya ci nasara a zaben shugaban kasa.

Idan babu dan takarar da ya samu wannan nasara a zagayen farko, za a gudanar da zabe zagaye na biyu a cikin makonni biyu da ‘yan takara biyu da suka fi samun kuri’u.

Duk da cewa an fi mayar da hankali ne a kan zaben shugaban kasa, amma masu zaben za su jefa kuri’a a zaben ‘yan majalisa da kuma wakilan gundumomi. Wasu daga cikin masu sharhi sun yi hasashen cewa akwai yiwuwar za a yi matukar gumurzu a zaben shugaban kasa.

Sun bayyana cewa Jam’iyyar ZANU-PF ta ci gaba da kasancewa cikin rudani duk da irin bakin jinin da ta yi musamman a birane.

Mai jagorantar jam’iyyar ya kasance mutum ne na dauri wanda ya dauki makami domin yaki don samun ‘yancin kan kasa inda tun lokacin samun ‘yancin kan kasar yake gwagwarmaya.

“Irin tsohon labarin da aka saba ji ne. Maimaici ba tare da sauyi ba. Ta fuskar zamantakewa, tattalin arziki da kuma siyasa. Babban abokin adawar ba zai iya kada ZANU-PF a yanzu ba,” kamar yadda Alexander Rusero wanda mai sharhi ne kan harkokin siyasa da yake zaune a Zimbabwe ya shaida wa TRT Afrika.

Zimbabwe ta dade tana fama da matsin tattalin arziki. Hoto/Others

Abin da ake bukata a halin yanzu

A halin da ake ciki a yanzu na rashin aikin yi da kuma yadda darajar kudin kasar ke raguwa da karin kudin kayayyaki, halin da tattalin arzikin kasar yake ciki a halin yanzu wani abin damuwa ne ga masu zabe.

Wani bincike wanda aka wallafa a watan Yunin da ya gabata da kamfanin bincike na Afrobarometer ya yi ya nuna cewa mutum biyu cikin goma na kasar ne kadai suke da yakinin cewa abubuwa za su gyaru ba tare da bata lokaci ba.

Wadanda suka amsa tambayoyin sun bayar da sakamako mara kyau kan gazawar gwamnati wurin daidaita farashi da samar da ayyukan yi da inganta yanayin rayuwa da tafiyar da tattalin arziki.

“Mutane kadan ne suka yi hasashen cewa tattalin arzikin zai gyaru inda da dama suka bayyana yanayin rayuwarsu na cikin wani hali. ‘Yan kasa sun ba gwamnati maki kadan kan batun tattalin arziki da samar da ayyukan yi,” in ji rahoton.

Binciken ya kara da cewa alkawuran da Mnangagwa ya yi kan fito da sabbin tsare-tsare domin farfado da tattalin arzikin kasar sun kasance wani lamari mai wahala.

“Rashin gaskiya ne a ce Mnangagwa bai yi komai ba. Mun ga sauyi ta wasu bangarori a cikin gida da waje,” in ji Rusero.

Zimbabwe ce kasar da ta fi kowace kasa arzikin Lithium a Afirka, wanda sinadari ne wanda ake amfani da shi wurin yin batira masu caji na motoci.

Kasar na da burin samar da kashi 20 cikin 100 na sinadarin a fadin duniya. Sai dai akwai damuwa kan cewa fitar da Lithium din zai kasance wata dama da aka rasa sakamakon kasar tana fitar da platinum da diamond amma hakan ba ya nunawa a hidimar jama’a.

Masu zabe a kasar za su zabi shugaban kasa da 'yan majalisa. Hoto/Others

Zaben gaskiya da adalci

Yakin neman zaben da ake yi ya cika da rudani da kuma goyon baya daga shahararru. Shahararren dan wasan damben nan na Amurka Floyd Mayweather ya hau jirgi domin nuna goyon bayansa ga shugaba mai ci.

Haka kuma ya halarci daya daga cikin yakin neman zaben Jam’iyyar ZANU-PF. Sai dai duk da yakin neman zaben da ake yi, masu sharhi kan siyasa na cewa ana samun karuwar barazana ta siyasa da rikici.

An kashe wani mai goyon bayan Jam’iyyar CCC a farkon watan nan a lokacin wata arangama da magoya bayan jam’iyyar mai mulki. Sai dai ZANU-PF ta nesanta kanta daga wannan lamarin.

‘Yan sanda na ta toshewa da kuma tarwatsa gangamin siyasar ‘yan adawa. A wani lamarin, ‘yan sandan sun bayar da dalilai da suka hada da karancin ban-dakuna a wuraren gudanar da gangamin.

Babbar jam’iyyar adawar dai ba ta yi nasara ba inda ta nemi shiga da kuma tantance rajistar masu kada kuri’a. Hakan ya biyo bayan korafe-korafen da aka yi kan cewa an mayar da sunaye da dama na masu kada kuri’a a wuraren da ‘yan adawa ke da shi daga wuraren kada kuri’u na gargajiya.

Babbar jam’iyyar adawa ta kasar ba ta samu adamar samun rajistar masu kada kuri’a ba. Wannan ya biyo bayan korafe-korafen da aka samu masu yawa kan cewa an sauya sunayen masu kada kuri’u da dama na ‘yan adawa da aka sauya musu wuri daga inda suke zabe na asali.

Sai dai hukumar zaben Zimbabwe ta musanta wannan zargin inda ta ce za ta yi zaben gaskiya da adalci. Zimbabwe na da tarihin rikicin siyasa.

Sai dai hukumomi na cewa sun shirya wa zaben gaskiya. “’Yan sandan Zimbabwe sun dauki matakai masu yawa domin tabbatar da cewa an gudanar da zaben cikin lumana da gaskiya da adalci,” kamar yadda Shugaban ‘Yan sanda Tandabantu Godwin Matanga ya shaida.

TRT Afrika