Jam'ian tsaron Nijeriya na ikirarin samun nasara a farmakin da suke kai wa maboyar 'yan bindiga. Photo/Nigerian Army

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce ta soma farautar ‘yan bindigar da suka sace masallata 10 a garin Bushe na Sabon Birni da ke Sokoto.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Sokoto ya tabbatar wa ‘yan jarida a ranar Juma’a cewa ‘yan bindiga sun afka garin ne da sanyin asuba inda suka sace mutanen a lokacin da suke tsaka da Sallar Asubahi.

“Ina so na tabbatar muku da cewa rundunar ‘yan sandan Nijeriya tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro na aiki ba hutawa domin tabbatar da an ceto waɗanda aka sace nan take,” in ji Rufai.

Mazauna garin sun tabbatar da cewa daga cikin waɗanda aka sace har da limamin masallacin.

Haka kuma sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun ɗauki tsawon lokaci suna addabar su duk da cewa akwai jami’an tsaro a garin.

A ‘yan kwanakin nan, wasu daga cikin ƙauyuka a Sokoto na fuskantar rashin tsaro musamman ta hanyar hare-haren ‘yan ta’addan Lakurawa da sauran ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Ko a watan Janairun da ya gabata sai da ‘yan bindiga suka kashe sojoji biyar a Ƙaramar Hukumar Gudu da ke Jihar Sokoto.

TRT Afrika da abokan hulda