Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta mayar da martani dangane da hotunan wasu ‘yan bindiga da ke baje-kolin kuɗin fansa a shafukan sada zumunta.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi ne ya yi martanin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Ƙorafin da wani mai wallafa labarai dangane da tsaro @ZagazOlaMakama ya yi a shafinsa na X inda ya wallafa hotunan ‘yan bindigan tare da cewa yanzu har ta kai suna nuna kuɗin fansar da suke karɓa, hakan ya jawo Adejobi ya yi martanin.
“Ba za mu iya kama duka masu laifi a lokaci guda ba. Aƙalla a yaba mana dangane da waɗanda muka kama. Muna kama su a kullum, kuma masu yawa,” in ji Adejobi a martanin da ya mayar.
“Jami’an soji da ‘yan sanda na iya bakin ƙoƙarinsu. Ya kamata a rinƙa gani tare da yaba wa ƙoƙarin jami’an. Akwai buƙatar mu haɗa kanmu baki ɗaya domin magance matsalolin tsaro da wasu matsalolin a Nijeriya. Akwai tabbacin cewa babu wani mai laifi da zai ci bulus ba tare da an hukunta shi ba,” kamar yadda Adejobi ya ƙara da cewa.
Duka waɗannan na zuwa a daidai lokacin da a ‘yan kwanakin nan aka ga wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suna amfani da shafukan sada zumunta tare da tambayar lambobin asusun ajiya na jama’a domin ba su na goro.
Matsalolin 'yan bindiga masu garkuwa da mutane na daga cikin abubuwan da ke damun arewacin Nijeriya.
'Yan bindigar suna da sansanoni a dazukan jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, da Neja, inda suke kai mutanen da suka sace, ciki har da ɗalibai daga makarantu