Zuwa yanzu dai rundunar sojin Nijeriya ba ta ce komai ba dangane da kashe tsohon jami'in nata. / Hoto: Others

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce jami’anta sun soma bincike dangane da kashe Birgediya Janar Uwem Udokwere a gidansa da ke Abuja babban birnin ƙasar.

A sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce an kashe janar ɗin mai ritaya a safiyar Asabar yayin wani hari da ‘yan fashi da makami suka kai a gidansa da ke rukununin gidaje na Sunshine Homes a unguwar Lokogoma a Abuja.

“Dangane da mummunan harin da aka kai rukunin gidajen Sunshine wanda ‘yan fashi da makami suka kai wanda ya yi sanadin mutuwar Birgediya Janar Uwam Harold Udokwere mai ritaya a ranar 22 ga watan Yunun 2024, da misalin 03:00 na asuba, kwamishinan ‘yan sandan birnin tarayya CP Beneth C. Igweh ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan yadda lamarin ya faru,” in ji sanarwar.

Kwamishinan ‘yan sandan ya jajanta wa iyalan mamacin inda ya ce za a yi ƙoƙarin ganowa da kuma ɗaukar matakai kan waɗanda aka kama da aikata wannan ta’asar.

Haka kuma kwamishinan ya jaddada cewa za su ci gaba da ƙoƙari wurin tabbatar da tsaro da kuma yaƙi da masu aikata muggan laifuka a birnin tarayyar.

Abuja na daga cikin wuraren da ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane ke kai hare-haren a ‘yan kwanakin nan, duk da cewa jami’an tsaro suna cewa suna ƙoƙarin daƙile ‘yan fashin.

Ko a ‘yan kwanakin nan sai da ‘yan sandan suka ce sun kashe ‘yan bindiga uku a Abuja da kuma gano makamai.

TRT Afrika