Rundunar 'yan sandan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ta sanya dokar hana fita ta awa 24 a fadin jihar domin dakile duk wata barazana ta tsaro.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Mohammed Usaini Gumel ne ya bayyana haka a jawabin da ya gabatar ga manema labarai ranar Laraba.
Rundunar 'yan sandan ta dauki matakin ne jim kadan bayan kotun sauraren kararrakin zaben jihar ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin zababben gwamnan jihar.
Kotun ta bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ya sauka daga kan mulki sannan ya mika takardar shaidar cin zaben gwamna a 2023 ga Nasiru Gawuna.
Hakan ne ya sa aka soma zaman dar-dar a fadin jihar domin tsoron abin da ka je ya komo.
Kwamishina Gumel ya ce sun sanya dokar hana fita "daga karfe shida na yamma (ranar Laraba) zuwa karfe shida na yamma (ranar Alhamis)" domin tabbatar da nauyin da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya dora musu na wanzar da tsaro.
Ya ce sun jibge jami'an tsaro a ko'ina ciki har da hanyoyin shiga da kuma fita daga jihar ta Kano domin dakile duk wata barazana ta tsaro.
"Muna sanar da mazauna Kano cewa an aika da gamayyar jami'an tsaro zuwa kowane lungu da sako na jihar nan ciki har da mashiga da mafitar jihar domin tabbatar da tsaro da bin dokar hana fita ta awa 24 da gwamnatin jihar ta sanya," in ji Kwamishinan.
Sai dai ya kara da cewa za a bar masu ayyukan gaggawa irin su likitoci da 'yan kwana-kwana da makamantansu su yi zirga-zirga.