Sokoto na daga cikin jihohin da ke fuskantar hare-haren 'yan bindiga. / Hoto: Reuters

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce tana gudanar da bincike kan batun wani hari da ‘yan bindiga suka kai a Ƙaramar Hukumar Gwadabawa da ke Sokoto.

A jajibirin sallah ne ‘yan bindigar suka kai hari ƙauyen Tudun Doki inda suka kashe aƙalla mutum shida da kuma garkuwa da mutane da dama.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Sokoto Ahmed Rufa’i ya tabbatar da harin inda ya ce tuni aka gano gawawwaki shida, sai dai ‘yan sanda ba su da tabbacin adadin mutanen da aka sace.

Jihar Sokoto da ke arewacin Nijeriya na yawan fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa inda suka kashe ɗaruruwan mutane a jihar a shekarun nan.

Ƙarin hare-hare

A watan Maris, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 15 daga wata makaranta a Sokoto a wani hari da suka kai da asuba, kwanaki kaɗan bayan an sace ɗalibai kusan 300 daga Jihar Kaduna mai maƙwabtaka da Sokoton.

A watan Maris, sojojin Nijeriya sun yi ƙoƙari domin daƙile wani hari da ‘yan bindigar suka kai a Damba Dikko da ke Ƙaramar Hukumar Illela ta Jihar Sokoto.

’Yan bindigar suna da sansanoni ne a katafaren dajin da ya ratsa jihohin Zamfara, Katsina, Kaduna, da Neja.

A watan da ya gabata, ’yan bindigar sun kai farmaki kauyuka hudu a Ƙaramar Hukumar Sabuwa ta jihar Katsina, inda suka kashe mutane 25, galibi ‘yan banga na yankin, a wani mataki na ramuwar gayya kan farmakin da sojoji suka kai maboyarsu, in ji jami’an yankin.

TRT Afrika