SP Wakili ya ce idan suka samu Dr Dutsen Tashi za su miƙa shi ga kotu ne. Hoto: Others

Rundunar 'yan sandan Jihar Bauchi da ke Nijeriya ta ce tana neman fitaccen malamin nan na addinin Musulunci Dr. Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi ruwa-a-jallo.

Mai magana da yawun rundunar, SP Ahmad Muhammad Wakili ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa suna neman malamin ne saboda raina kotu, inda ya kara da cewa za a bayar da tukwuici mai tsoka ga duk wanda ya taimaka aka kama shi.

Duk da cewa SP Wakili bai yi wa TRT Afrika Hausa karin bayani a kan laifin da ya sa kotu ke neman Dr Dutsen Tanshi ba, saboda a cewarsa ba zai iya magana a kai ba tun da batun yana kotu, rahotannin baya sun nuna cewa kotun na tuhumarsa ne da tada hankulan jama'a.

Ya ce kuma ce sun je gidan malamin nemansa amma ba su same shi ba, wanda hakan ne ya sa suka saka cigiyarsa a shafukan sada zumunta.

Ko da TRT Afrika Hausa ta tambayi jami'in ƴan sanda abin da za su yi masa idan suka same shi, sai SP Wakili ya ce za su miƙa shi ga kotu ne.

"Mu babu ruwanmu ba riƙe shi za mu yi ba, umarnin kotu muke bi a matsayinta na hukumar Nijeriya. Da zarar mun same shi za mu kai shi ga kotu," ya ce.

TRT Afrika