Masu sanya ido sun jaddada muhimmancin wanzar da zaman lafiya da kuma amincewa da sakamakon karshe na zaben. Hoto: Reuters  

'Yan Laberiya suna kada kuri'unsu a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a yau Talata don zabar wanda zai jagoranci kasar tsakanin tsohon dan kwallon kafa George Weah da ke neman wa'adi na biyu da kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai.

Mutanen biyu sun taba fafatawa a zaben shugaban kasa a shekarar 2017 inda Weah ya yi nasara a zagaye na biyu da sama da kashi 61 cikin dari na kuri'un da aka kada.

A zagayen farko na zaben da aka gudanar a ranar 10 ga watan Oktoba, Weah, mai shekaru 57 da Boakai, mai shekaru 78 sun gaza samun kashi 50 cikin dari na kuri'un da aka kada, ko da yake Weah na gaba da kuri'u 7,126.

Zaben na bana shi ne na farko tun bayan kawo karshen aikin Majalisar Dinkin Duniya MDD a shekarar 2018 na wanzar da zaman lafiya a kasar Laberiya, wanda aka soma bayan mutuwar fiye da mutane 250,000 a yakin basasa guda biyu da kasar ta fuskanta tsakanin shekarar 1989 zuwa 2003.

Masu sanya ido sun jaddada muhimmancin wanzar da zaman lafiya da kuma amincewa da sakamakon karshe na zaben.

"Ba shakka zabukan shekarar 2023 na wakiltar wani muhimmin mataki na tabbatar da zaman lafiya da dimokuradiyya a Laberiya, da ma yankin baki daya," a cewar wata sanarwa ta MDD .

Sama da mutane miliyan 2.4 ne suka yi rajistar zabe, inda aka bude rumfunan zabe da misalin karfe 8:00 na safe (0800 GMT) zuwa karfe 6:00 na yamma (1800 GMT).

TRT Afrika