Rundunar 'yan sandan Zamfara ta ce ta tura tawagar ƙwararrun jami'anta domin kuɓutar da Rabarand Father Mikah Suleiman cikin ƙoshin lafiya./Hoto:Reuters

Hukumomi a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya sun tabbatar da sace wani malamin cocin St. Raymond Catholic da ke yankin Damba na birnin Gusau, Rabarand Father Mikah Suleiman.

Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce an sace malamin cocin ne a daren Asabar a gidansa da ke unguwar Damba a birnin Gusau, kamar yadda gidan talbijin mai zaman kansa Channels TV ya ruwaito.

Ya ƙara da cewa ba a kai musu rahoto game da sace malamin cocin ba amma rundunar 'yan sanda ta tura tawagar ƙwararrun jami'anta domin kuɓutar da shi cikin ƙoshin lafiya.

“Tabbas, wannan lamari ya faru a daren ranar Asabar, inda waɗansu masu garkuwa da mutane suka sace Rabarand Father a gidansa. Ba a ba mu bayani ba lokacin da lamarin ya faru amma na fahimci cewa yana zaune ne shi kaɗai ba a coci ba,” in ji shi.

Wani babban malamin cocin Katolika ta Sokoto, Very. Rabaran Father Nuhu Iliya, a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, ya yi kira ga Kiristoci su duƙufa wajen addu'a don Allah ya kuɓutar da Rabarand Father Mikah Suleiman.

Jihar Zamfara ta daɗe tana fama da hare-haren 'yan bindiga inda suka sace dubban mutane, ciki har da ɗalibai a makarantunsu. Gwamnatoci daban-daban sun sha alwashin kawo ƙarshen matsalar, sai dai har yanzu lamarin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

TRT Afrika