Wasu mahara dauke da makamai sun kai hari a wani sansanin soji da ke kauyen Nahuta a Jihar Katsina, inda suka fatattaki sojoji suka ƙona motocinsu, sannan suka yi sata a shaguna da gidaje, kamar yadda wani mazaunin garin da majiyoyi biyu suka bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Litinin.
Harin da aka kai a sansanin sojoji inda sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ke zama a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina, ya faru ne da yammacin ranar Lahadi, a cewar wani mazaunin garin Isa Bello.
Sai dai kokarin jin ta bakin mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Abubakar Sadiq ya ci tura. Amma wani jami’in gwamnatin jihar Katsina ya tabbatar wa Reuters cewa ba a samu asarar rayuka ba a kauyen.
Majiyoyin da jami’in sun nemi a sakaya sunansu saboda ba su da izinin yin magana da manema labarai.
A shekara ukun da suka wuce 'yan bindiga sun yi barna sosai a yankin Arewa maso yammacin Nijeriya, inda suka yi garkuwa da dubban mutane, tare da kashe daruruwa da kuma hana tafiye-tafiye ko yin noma a wasu yankunan.
Bello ya ce ‘yan bindigar wadanda suka zo kan babura da wata babbar mota da misalin karfe 10 agogon GMT, sun mamayi sojojin ne bayan musayar wuta na tsawon sa’o’i uku.
Wata majiyar tsaro ta ce maharan sun kona motoci da wasu kadarori a sansanin, sannan suka zarce zuwa kauyen Nahuta inda suka yi sata a shaguna da gidaje tare da sace kayayyaki da dabbobi na miliyoyin naira.
Harin da aka kai a sansanin sojoji ya haifar da firgici a tsakanin mazauna garin Nahuta, da dama daga cikinsu sun gudu zuwa kauyukan da ke kusa da su domin neman mafaka, in ji Bello.