Wani hari da 'yan a-waren Kamaru suka kai a wani kauye da ke yankin da ake magana da Turancin Ingilishi ranar Litinin ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 20, ciki har da mata da kananan yara, a cewar gwamnatin kasar.
Minista a Fadar Shugaban Kasar Mengot Victor Arrey-Nkongho ya shaida wa gidajen rediyo cewa an kai harin da daddare a kauyen Egbekaw da ke yammacin kasar, inda dakarun gwamnati da masu neman ballewa daga Kamaru suka kwashe fiye da shekara bakwai suka ba-ta-kashi.
"Wadanda aka kashe sun hada da maza da mata da kananan yara, kuma sun zarta 20. Ba za mu amince da wannan ta'asa ba," in ji ministan.
"Da tsakar dare 'yan ta'adda dauke da bindigogi da kananan makamai suka bude wuta a kan jama'a," a cewar wani jami'in yankin mai suna Viang Mekala a hira da wani gidan rediyon kasar.
Labari mai alaka: Yadda 'yan a-waren Kamaru suka 'kashe tare da kona matata da 'ya'yana'
Ya tabbatar da cewa: "an kashe mutum fiye da 20 sannan aka jikkata mutum bakwai, kana an kona gomman gidaje."
Yankunan arewa maso yamma da kudu maso yammacin Kamaru da ke magana da Turancin Ingilishi sun fada rikici tun bayan da suka ayyana ballewa daga kasar a 2017.
Rikicin ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 6,000 sannan ya tilasta wa sama da mutum miliyan daya tserewa daga gidajensu, a cewar kungiyar kare hakkin dan'adam ta International Crisis Group.
Shugaba Paul Biya, mai shekara 90, wanda ya kwashe shekara 41 yana jagorantar Kamaru, ya ce ba zai amince wani yanki ya balle daga kasar ba.