A karon farko bayan watanni 20 da soma yaƙi, fararen hula a yankin kudancin Sudan da yaƙi ya ɗaiɗaita sun karɓi ayarin motoci da ke ɗauke da kayayyakin abinci.
Jumullar manyan motoci 28 ne suka isa yankin Jebel Awliya da ke kudu da birnin Khartoum, kamar yadda sashen bayar da agajin gaggawa na na wata kungiyar sa kai da ke gudanar da ayyukan agaji na farko a fadin kasar Sudan ya bayyana.
Ayarin dai ya hada da tireloli 22 dauke da abinci daga hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP, da wata tirela daya daga ƙungiyar likitoci ta MSF da kuma tireloli biyar ɗauke da magunguna daga hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF.
Tsananin yunwa
Jebel Awliya dai na daya daga cikin yankuna da dama a fadin kasar Sudan da ke fuskantar matsalar yunwa bayan da bangarorin da ke fada da juna suka toshe hanyoyin shiga yankin.
Tun lokacin da aka fara yakin a watan Afrilun 2023 tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, babu abin da ya shiga ko fita ba tare da amincewar bangarorin biyu ba.
Ƙungiyar sa kai ta ERR Volunteers ta shafe watanni tana shiga tsakani, inda ta jure barazana da tarzoma domin ta samun damar shiga yankin.
"An toshe hanyar shiga yankin da saboda yanayin rikice-rikice," in ji wakilin UNICEF na Sudan Sheldon Yett, inda ya ƙara da cewa an kwashe watanni uku ana tattaunawa don ganin an bar ayarin motocin sun shiga.