Harin ya faru ne a kusa da wani sanannen gandun daji . Hoto / Reuters  

Wata uwa ta ceto ɗanta mai shekaru biyu daga bakin wata damisa a yankin arewacin Zambiya,

Kasar na ɗaya daga cikin matsugunan namun daji a Afirka inda ake sake fuskantar wani sabon tashin hankali tsakanin namun daji da ƴan'adam.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata a wani ƙauye mai suna Nabwalya Chiefdom, da ke kusa da Gandun Dajin Luangwa ta Arewa, wanda ke da dimbin namun daji na a Afirka.

A yanzu haka yaron yana jinyar munanan raunuka da ya samu a Babban Asibitin Ofishin Jakadancin Chilonga a gundumar Mpika, inda kauyen Nabwalya yake.

Mahaifiyarta yaron Tidah Mubanga, ta ce harin ya faru ne a lokacin da suke barci a gonarsu.

Tsari

Mubanga ta ce ta ankara ne lokacin da ta ji dabbar tana kokarin janye yaronta ta kansa, daga nan ta soma jan yaron daga bakin dabbar har ta samu nasara.

Babban Likitan Asibitin 'Chilonga Mission' Bertin Kalengai ya ce da ana karbar majinyacin, aka yi kokarin dakatar da jinin da ke zuba daga jikinsa tare da ceto rayuwar yaron.

Likitan ya ara da cewa, a halin da ake ciki yaron ya fita daga cikin hatsari kuma yana samun kulawa sosai.

Dakta Kalengai ya ce wannan shi ne karo na uku a shekarar nan da aka samu rahoton hare-haren namun daji a asibitin daga Nabwalya.

Yana mai cewa sauran biyun da aka kawo asibitin sun gamu da harin cizon kada, kuma dukka wadanda suka jikkata na samun sauki a asibiti.

Dakile hare-hare

Hakimin kauyen Mpika David Siame ya ziyarci yaron a ranar Laraba, yana mai tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa za su yi aiki tare da sashe gandun daji da namun daji na kasar don ganin an dakile hare-haren.

"Ina sane da cewa mutanenmu na rayuwa cikin fargaba saboda hare-haren dabbobin nan, amma ba wai gwamnati ta yi kunnen ƙashi ga lamarin Nabwalya ba ne. Muna aiki kan matakan dakile hare-haren," in ji shi.

TRT Afrika