Daga Mamadou Thiam
Sannu a hankali al'amuran yau da kullun sun fara daidaita a Dakar, babban birnin kasar Senegal, bayan zanga-zangar da magoya bayan madugun 'yan adawa Ousmane Sonko suka shafe tsawon kwanaki suna gudanarwa a makon jiya.
Zanga-zangar ta biyo bayan hukuncin daurin rai-da-rai da kotu ta yankewa Sonko, kan laifin “gurbata matasa”, ko da yake an wanke shi daga laifin fyade.
Akalla mutane 16 ne suka mutu a arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar da 'yan sanda, a cewar hukumomi.
A tashe-tashen hankula da hargitsi da birnin Dakar ya fuskanta, ‘yan daba sun kai hari Jami'ar Cheikh Anta Diop, jami'ar da aka fi girmamawa a Senegal, inda suka barnata wurare da dama tare da tilastawa dalibai barin makarantar.
Kawo yanzu ba a san ainihin ko su wane suka kai harin ba da kuma dalilansu na kai wa jami'ar hari ba. Hukomomi sun bayyana su a matsayin ''mutane da ba a tantance su ba''.
Shugaban jami'ar, Amadou Aly Mbaye ya shaidawa TRT Afrika, "Jami'ar cibiya ce ga al'ummar kasa.
"Akwai mutane daga kowane bangare na siyasa da addini a can, kowa na bukatar ilimi. Ba a san takamaiman abin da ya faru ba".
"Dukkanmu mun yi bakin ciki ganin yadda jami'ar ta koma. Kamar yadda aka lalata jami'ar Cheikh Anta Diop, haka ma aka lalata jami'ar Ziguinchor," in ji ministan ilimi mai zurfi na Senegal, Farfesa Moussa Baldé.
"Abin da muka gani a nan shi ne aikin wasu mutane da manufarsu ita ce durkusar da jami'o'in Senegal, da karya lagon jami'ar Cheikh Anta Diop, wacce ke zama wata alama ta izzar Senegal da Afirka," in ji Ministan yayin da ya ke zantawa da manema labarai a ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru.
Adadin asarar da aka samu
Jami'ar Cheikh Anta Diop na daya daga cikin tsaffin jami'o'i a Afirka. A tsawon shekaru, ta samar da akalla shugabannin kasa hudu na Senegal.
Farfesa Moussa Balde ya koka cewa, ''Jami'ar tana daga cikin wurare da ake so a kai wa hari''.
Yanzu haka dai jami'ar na lissafa asarar da ta yi bayan an lalata gine-gine da motoci da muhimman takardu.
“Sashen gudanarwa da adana bayanan koyarwa duk sun kone, tare da bangaren ajiye bayanan daliban da suka kammala karatu, musamman ma sashen koyar da ilmin likitanci da tsangayar fasaha ta al’umma,” in ji Farfesa Amadou Aly Mbaye, shugaban jami’ar.
‘Yan daban sun kuma lalata wasu kayayyaki da ke harabar bangaren ilimin zamantakewa na jami’ar, inda motocin bas da ofisoshi suka kone kuma aka rushe ginin wajen.
"Cikin bakin ciki muka ga duk irin barnar da aka yi a jami'ar Cheikh Anta Diop," Maguette Sène, daraktan cibiyar walwala da dabaru na jami'ar ya shaida wa TRT Afrika.
“A harabar sashin ilimin zamantakewa na jami’ar, an kona babban ofishin wajen, an kuma yi awon gaba da wasu kayayyaki. Sannan an yi wa ofisoshin abokan aikinmu fashi.
Shi ma zauren Omar Pène, wanda aka bude ’yan watannin da suka gabata, an kwashe duk kayayyakin da aka zuba a ciki. Yanzu haka an mayar da wajen mara amfani,” inji shi.
Dalibai sun tsere
“Sun kuma kona motocin bas da ake debo ma’aikata guda takwas. Babban abin takaicin kwasar ganimar shi ne lalata muhalli da aka yi.
"Mun ga yadda aka tumbuke bishiyoyi, hakan ya nuna cewa niyyarsu su durkusar da jami'ar ne," in ji shi.
Jami’ai sun tabbatar da cewa an lalata wata sabuwar katangar jami’ar, amma har yanzu ba a kai ga tantance adadin barnar da aka yi ba.
"Muna kan aikin kidayar barnar da aka yi mana, kasancewar ba a kammala aikin ba, ba za mu iya bayyana ainihin yawan barnar ba," in ji Amadou Aly Mbaye.
“An shigar da kara domin gano wadanda suka aikata wannan aika-aika, amma har yanzu muna ci gaba da bin diddigin lamarin, kuma idan lokaci ya yi, za mu yi magana da jama’a don ba da cikakken kiyasin irin barnar da aka yi." in ji shi.
Biyo bayan tashin hankalin, Jami'ar Cheikh Anta Diop ta kasance babu kowa a yayin da dalibai suka gudu domin samun mafaka.
Ousmane, wani dalibi a jami’ar ya shaida wa TRT Afrika, “Ina zaune a Pavillon À, wanda shi ne bangaren jami’ar da ke gaba-gaba saboda yana fuskantar babbar kofar shiga cikin makarantar.
A duk lokacin da aka samu wani yamutsi mu ne kan gaba wajen shan wahala. Na yi sa’a na fita kafin abubuwa su runcabe".
Rikicin dai ya kawo cikas ga karatun dubban dalibai. “Mu dalibai da ba mu da ‘yan uwa a Dakar, mu ne lamarin ya fi shafa.
"An tilasta min barin garin don komawa ga iyalai na da suke arewacin Senegal mai nisan kilomita 500,” in ji Adama Sow, wata daliba da ke aji biyu a shekarun karatunta wacce ta fito daga yankin Matam.
"Ina jira in ga matakin da hukumomi za su dauka kafin na dau matsayar komawa Dakar," in ji dalibar.
Dole a ci gaba da karatu
Fusatattun ‘yan daban sun kuma kai hari tare da kwashe kayayyaki na sashen da ke koyar da aikin jarida, da ilimin kimiyyar sadarwa, da fasaha da kuma kona motoci da wani bangare na ginin.
Farfesa Moussa Baldé, ministan ilimi mai zurfi ya sha alwashin cewa, "Za a gudanar da bincike tare da hukunta wadanda suka aikata laifin".
An yi ta kiraye-kirayen cewa a samar da ingantaccen tsaro a cibiyoyin ba da ilimi bayan tashin hankalin.
"Za a dauki lokaci mai tsawo kafin a gyara duk wani abu da aka sace ko aka lalata. Amma jami'ar za ta ci gaba da kasancewa a tsaye. Muna da kwarin gwiwar za mu iya tashi mu ci gaba da gudanar da ayyukanmu.
"Ya kamata mu mai da hankali kan tsarin tsaron mu, kuma na yi imanin hukumomi na da ikon daukar matakan da suka dace, "in ji daraktan jami'ar, Maguette Séne.
A cikin wata sanarwa da hukumar gudanarwar jami'ar ta fitar, an dakatar da ayyukan karatu ''har sai an sake fitar da wata sanarwa''.
Ministan ilimi mai zurfi, Farfesa Moussa Baldé, ya umarci hukumomin jami'ar da su yi amfani da zabin karantarwa ta intanet wajen koyar da dalibai, yana mai ba da shawarar cewa ka da a bar wani gibi da zai nuna nakasun da aka samu sakamokon wannan lamari.