Juma Masoud ya waiwaya baya yana tuno wasu kananan abubuwa da yawancin mutane suke dauka da wasa, amma kuma sun gagare su.
"Hatta sanya danka a makaranta abu ne mai wuya. Ina rayuwa ne kamar bako a cikin gidana. Ba a maraba da ni a ko ina. Ba na iya yin abubuwan da nake bukata," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Dangin Juma sun kasance a kasar Kenya kimanin shekaru 200 da suka wuce, ko da yake a hukumance ya kasance "ba shi da matsayin dan kasa a kowace kasa a duniya (stateless)" ku san galibin rayuwarsa.
A ranar 28 ga watan Yulin bana, Shugaba William Ruto ya ba Juma da iyalansa da kuma wasu mutum 7,000 'yan asalin tsibirin Pemba abin da ya fi muhimmanci a gare su — wato samun matsayin zama kabila a kasar Kenya da kuma zama 'yan kasar wacce take yankin gabashin Afirka.
"Ina cikin farin ciki a yanzu, kuma ina jin dadin cewa yanzu zan iya shiga ko ina kamar sauran 'yan Kenya," in ji Juma.
"Batun gaskiya wannan nasara ce ga kakannina da jama'ata, wadanda suka zo Kenya kimanin shekaru 200 da suka wuce."
Juma yana rayuwa ne tare da matansa biyu da 'ya'yansa bakwai a wani karamin gida a Mayongu a lardin Kilifi a gabar tekun Kenya. A baya yana fargabar makomar 'ya'yansa musamman idan ya bar su da irin rayuwar da ya taso a ciki.
"Abu ne ba ka nan ba ka can," kamar yadda ya bayyana lokacin da ya tuna baya, inda ya tuna da muradan al'ummar Pemba.
Tsibirin kadaici
A harshen Swahili, baki wadanda suka danganta asalinsu da Pemba, wato daya daga cikin tsibiran Zanzibar wanda yake kunshe cikin kasar Tanzaniya, ana kiransu da sunan Wapemba.
Yayin da Juma a ko da yaushe ya san inda asalinsa yake, bai taba tunanin ya kwashe kayansa ya koma tsibirin da kakanninsa suke ba.
"Tana iya yiwuwa ina da wasu dangi a can, ba ka sani ba," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
"Sai dai babu wanda na sani a can. Kakannina sun koma Kenya shekaru masu yawa da suka wuce. An haifi mahaifina ne a Kenya. Ni ma kuma an haife ni ne a Kenya. Wannan ne abin da na sani."
Yayin taron da aka bai wa mutane da dama takardar shaidar zama 'yan kasa, Shugaba Ruto ya ce al'ummar Pemba ta sha wahala sosai ba tare da amincewa da su a matsayin 'yan kasa ba.
"Tsawon shekaru, suna rayuwa a nan ba tare da takardun zama 'yan kasa ba, kuma sun shiga mawuyacin hali saboda haka," in ji shi, "daga yau, Wapemba za su samu shaidar zama 'yan Kenya."
A wani yanayi na farin ciki da annashuwa, kwalla ta cika idon Juma da sauran mutane.
"Wannan farin cikin ya wuce batun takardar shaida ta ID card ko takardar haihuwa," in ji shi.
"Wannan yana nufin al'ummar Pemba za su samu damar kai yaransu makaranta da asibiti da damar yin aiki, duka wadannan a baya ba za mu iya yinsu ba."
Rayuwar buya
Har sai lokacin da suka samu shaidar zama 'yan kasa da damar yin rayuwarsu cikin mutunci, Juma da sauran al'ummomi sukan kasance cikin tsoro da tsangwama duk da cewa yawancinsu an haifi su ne kuma sun girma ne a Kenya.
"A shekarar 2017, an kama ni a gidana. 'Yan sanda sun kama ni bayan da suka same ni da takardar shaida (ID card) ta jabu," in ji shi.
"An tsare ni a ofishin 'yan sanda tsawon kwana 15. Ko bayan da aka sake ni an bukaci da na rika kai kaina ofishin 'yan sanda sau daya a kowane mako har tsawon watanni shida. Abin ya taba kimata."
Saboda farmakin da 'yan sanda suke kawowa kowane mutum da ya kai shekara 18, za ka ga mutane suna guduwa suna buya idan suka ga 'yan sanda. Saboda yawan kama mutane da ake yi da muzanta su ya sa rayuwarsu ta tagayyara.
"A wasu lokuta, muna amfani da takardar shaidar (ID card) din wasu ne idan muna bukatar wani abu, kodayake hakan laifi ne kuma yana tattare da hadari. Idan aka gano za a kama ka," in ji Juma.
Wasu al'ummomi sun gwammace su yi wa 'ya'yansu rijista da iyalan da ke da takardar shaidar zama 'yan kasa saboda su samu damar shiga makaranta. Ya ce sun gode wa Allah, yanzu duka wannan ya kau.
"Yanzu, 'ya'yanmu za su rike ID card dinsu cikin alfahari da takardar haihuwarsu mai dauke da sunansu," in ji Juma.
Yabo daga Majalisar Dinkin Duniya (MDD)
Kwamishinan Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya yana cikin mutanen da suka yaba wa Kenya dangane da daukar wannan matakin na amincewa da al'ummar Pemba a matsayin 'yan kasa.
"Na so a ce ina wajen don na gode wa Kenya saboda daukar wannan muhimmin matakin na bai wa al'ummar Pemba matsayi," kamar yadda aka bayyana a sakon kwamishinan Filippo Grandi, a shafinsa na Twitter.
"Wannan misali ne mai kyau ga wasu kasashe," in ji shi.
Kamar yadda Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta bayyana mutumin da ba shi da kasa shi ne wanda a doka ba shi da shaidar zama dan kowace kasa.
An haifi wasu mutane ba su da matsayin zama 'yan kowace kasa, yayin wasu suke rasa matsayinsu saboda wasu dalilai. Abin mamaki, yawancin mutanen da ba su da kasa suna rayuwa ne a kasashen da aka haife su.
Hukumar UNHCR ta yi kiyasin akwai mutum 10 a fadin duniya wadanda ba su da matsayin zama 'yan kowace kasa, ciki akwai kusan mutum miliyan daya a Afirka.
A Kenya, kasar tana da yawan jama'a da ya kai miliyan 50, tana da al'ummomi 44 da aka yi wa rijista, kafin a yi wa al'ummar Wapemba wacce ta zama ita ce ta 45 a jerin.
Bayanan Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa akwai mutum 18,000 marasa matsayin 'yan kasa a Kenya, tun bayan da aka ba al'ummar Makonde matsayin 'yan kasa a shekarar 2016.
Wasu al'ummomi da aka ba su matsayin 'yan kasa a Kenya a baya-bayan nan sun hada da wasu 'yan asalin Indiya da kuma Somaliya.