Daga Sylvia Chebet
Karkanda wata dabba ce mai girman gaske, tana da fatar jiki mai kama da sulke, sannan nauyinta ya kai kilogiram 3,500, amma duk da haka tana da ƙarfin iya gudu fiye da kilomita 54 cikin awa ɗaya.
Bisa nauyi da kuma gudun dabbar yasa aka daura ta akan sikelin ƙarfi na fam 8,000, wanda ya yi daidai da gudun mota.
A tsakanin manyan namun daji kuwa, ƙarfin karkanda ya ninka na zaki har sau goma.
Ko, wasu irin abubuwa ne suka bambanta wannan dabbar da suka sa take da rauni a wajen mafarauta duk da yanayin halittunta masu ban mamaki ?
Ƙahon karkanda ya samar da tarin arziki a haramtacciyar kasuwan duniya na siyar da sassan namun daji sannan wasu ƙungiyoyin farautar dabbobin suna samun riba wajen ƙauce bin matakan kariya don samun waɗannan manyan dabbobi.
A gandun Solio Ranch Game Reser, mai zaman kansa da ake kula da namun daji ya kasance matsuguni ga kusan kashi 30 cikin 100 na karkanda a Kenya, a yanzu haka sabon fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI na fafatawa da ayyukan masu farauta.
Asusun tallafawa namun daji na duniya WWF ya samar da ƙyamarori kirar 'FLIR thermal cameras' masu iya jure zafi kana masu fasahar AI da za su iya ɗauko ko wane iri abu a gandun dajin Salio, waɗanda aka ɓoye su tsakanin manyan kwarin duwatsun Kenya da kuma can cikin dajin Aberdare domin kare baƙaƙen karkanda da ke rayuwa a yankin.
An sanya waɗannan na'urori ne akan wani yanki na shingen gandun dajin mai kadada 49,000 wanda ake ganin yana da rauni wajen kai kutse daga mafarauta.
Ƙyamarorin FLIR thermal suna iya gano tare da jin duk giftawar wani abu kana su mayar da shi zuwa hoto.
Hakan zai ba su damar ''gani'' tare da bambance kowane irin yanayi a wurare daban-daban, cikin har da tsananin duhu da yahaki da hazo da zafi da sanyi har a cikin ciyayi.
"Wannan fasaha na kara inganta aikin gandun daji wajen cimma muhimmin aikin kare dabbar karkanda na Kenya." a cewar Mohamed Awer, babban jami'in Asusun WWF a Kenya
Rashin isassun kayan aiki
A cewar Colby Loucks, mataimakin shugaban shirin Asusun WWF kana daraktan Cibiyar sabbin fasahohi,ɗaya daga cikin manyan manyan ƙalubale ga masu mafarauta a namun daji a duniya shi ne ''ba sa taba isar su''.
''Muna buƙatar ƙarin jami'ai; abin da wannan fasaha ta (FLIR) ke yi shi ne tana iya ɗauko wasu wurare masu nisan kilomita a kullum a tsawon awannin 24, in ji shi.
Tare da taimakon manyan fasahohin, ayyukan jami'an gandun dajin -waɗanda galibi suke yin sintiri cikin ko wane irin yanayi ta ƙafa, a yanzu ya ragu sosai.
''Dukkan kyamarorinmu an haɗa su da fasahar AI kuna suna iya gaya maka ko mutum ne yake kusa ko kuma dabba ce. Bisa ga haka, na'urorin za su aika da sako ga jami'an,'' in ji Loucks.
An samar da wasu ɗakuna biyu da za ana kula da wannan aiki a Salio, inda ma'aikatan tsaron wurin ke kula da hotunan kai-tsaye daga ƙyamarori a duk dare da rana.
''A duk lokacin da aka samu wata barazana, jami'anmu na iya zuwa wurin cikin sauri, '' kamae yadda Kevin Carr- Hartley, babban daraktan gadun daji na Salio ya shaida wa TRT Afrika.
''Baya ga inganta yanayin aiki, kyamarorin FLIR suna taimaka wa wajen kare rayuwar jami'ai ta hanyar ba su muhimman bayanai game da inda za su shiga.''
Juriya da jajircewa
Dakta Erustus Kanga, babban darakta na ayyukan gandun namun dajin Kenya, ya yi imanin cewa aikin samar da tsoro ya shafi yin haɗin gwiwa.
''Ba mu yi asarar karkanda ko guda ɗaya ba a wannan wurin a tsawon shekaru shida da suka wuce. Hakan ya nuna jajircewarsu a nan Salio,'' kamar yadda ya shaida a wurin wani taron tunatarwa ta ranar jami'an gandun daji ta duniya a ranar 31 ga watan Yuli.
Tun da aka soma amfani da tsarin sa ido na AI a ƙarshen shekarar 2023, gadun dajin bai samu wani rahoto na kutsen masu farauta ba ko a katangar da aka shata musu ba.
''Salio ita ce wuri na uku a Kenya da ke da yawan Karkanda inda muka ba da tallafinmu wajen sanya ƙyamarorin FLIR.
Wuri na farko shi ne dajin Lake Nakuru a shekarar 2016, sai kuma OI Pejeta a shekarar 2020,'' in ji Geoffrey Chege , mai kula da shirin Karkanda na WWF a Kenya.
Ana hasashen cewa Meru National Park shi ne zai zama wuri na huɗu.
Tun farkon sanya kyamarorin shekaru takwas da suka wuce, ƙungiyoyi da ke yaki da masu farauta suka koyi wasu darussa a hanyar.
Ɗaya daga cikin muhimman abin da suka koya shi ne, buƙatar haɓaka hanyoyin samar da wutar lantarki don ci gaban aikin kyamarorin na FLIR fiye da kwanaki uku. ''A Salio, muna sarrafa ƙyamarorin ne ta hanyar amfani da makamashin hasken rana,'' Chege ya shaida wa TRT Afrika.
Ƙara ƙarfin aiki tsakanin jami'an da ke aikin sintiri yana da mahimmanci. "Fasaha tana da matukar amfani tamkar mutanen da suke amfani da ita,'' in ji Awer.
Manufar na kan hanya
Ƙungiyar Ƙungiyoyin Kare Halitta ta Duniya ta ayyana karkanda a matsayin wani nau'in dabba da ke cikin haɗari.
Lokacin da aka tsara shirin aiwatar da aikin alkinta karkanda na Kenya a shekarar 1983, wanda ya zarce adadin da aka yi niyya na karkanda 1,000, kamar ba zai yiwu ba, ko kuma ba za a iya cim ma wa ba.
"Al'ummar gabashin Afirka ta mayar da aiki da ake gannin ba zai yiwu ba zuwa wanda ya tabbata har ya ninka yawan karkanda zuwa 1,004 daga kasa da 400 a tsakiyar shekarun 1980,'' a cewar Chege.
''Muna kan hanyar cim ma burin Kenya na tsawon lokaci na kai ga yawan Karkanda 2,000 nan da shekara ta 2037.
"Yayin da muke bikin tuni da ranar Karkanda ta duniya a ranar 22 ga Satumba, na saɗaukar da nasarar da aka samu ga dukkan ƙungiyoyin kare Karkanda a faɗin ƙasar.''