Daga Eudes Ssekyondwa
Wata ranar ce da aiki ya yi yawa, a ma'aikatar Simons Uga a Entebbe da ke tsakiyar Uganda. Ma'aikata sanye da ƙananan riguna da wanduna masu ruwan ɗorawa mai haske suna kan gudanar da ayyukansu, suna wankewa da gogewa, da matsewa, da busarwa, da tantancewa da kuma auna ƴaƴan Vanilla.
Simons Musisi na sa ido a kan aiki tun daga farko har sai launin ƴaƴan Vanilla ya koma ruwan ƙasa mai baƙi-baƙi daga kore. Ya jima yana yin haka tun da ya kafa ma'aikatar a 2016.
Idan aka duba sosai za a lura cewa, kuzarin da aka saba ganin daraktan gudanarwar da shi ya gushe.
Cikin wani yanayi na damuwa, Musisi, fitaccen mai fitar da wake zuwa Amurka, yana ta nazarin yadda makomar harkar za ta kasance, duk da cewa ma'aikatansa suna aunawa da kuma ƙunshe kayan a cikin kwalaye domin fita da su.
"Wataƙila wannan ne karo na ƙarshe da zan tura da kaya Amurka," ya gaya wa TRT Afrika, kamar zai ƙware.
Sauyi na kankama
Amurka ta sanar a kwanan nan cewa za ta cire Uganda daga yarjejeniyar (AGOA) daga wata Janairu shekarar 2024.
Wacce aka ƙaddamar da ita a shekarar 2000, yarjejeniyar ta bai wa ƙasashen Afrika damar shigar da kaya kasuwanni Amurka ba tare da biyan kuɗin-fito ba.
Wannan abin damuwa ne a wajen ƴan kasuwar Uganda irin su Musisi, waɗanda suke fitar da ƴaƴan Vanilla mai nauyin tan 80 zuwa Amurka kowacce shekara, suna samun ribar kimanin dala Miliyan biyu.
"Idan aka ɗage sassaucin biyan kuɗin-fiton a ƴan watanni masu zuwa, za a tilasta wa abokan hulɗarmu su sayi vanilla a farashi mai tsada," a cewar Musisi. Tsakani da Allah, za su zaɓi su sayo kayan ne daga Madagascar, wacce take cikin yarjejeniyar ta AGOA. Abin zai shafe mu sosai."
Ƙasar ta Gabashin Afrika ita ce ta biyu mafi girma wajen fitar da ƴaƴan vanilla a nahiyar bayan Madagascar.
Duk da ƙasashen Afrika da yawa suna iya shigar da kayayyakinsu cikin Amurka ba tare da biyan kuɗin-fito ba, wasu masana na cewa, Amurka tana amfana da yarjejeniyar ta AGOA, tana amfani da ita a matsayin wata kafa ta manufofinta na ƙasashen waje, sannan kuma ta kwashe moriyar tattalin arziƙin nata.
‘"Kasuwanci ne tsakanin Amurka da take amfana sosai da kuma Afrika da take bayarwa da yawa, amma ta amfana da ƙasa da abin da ya kamata ta samu, Edward Wanyonyi, wani mai bincike al'amuran ƙasa da ƙasa mazaunin Kenya, ya faɗa wa TRT Afrika.
"Amurka ta fi amfana saboda galibin abin da Afrika take shigar wa kasuwanninta ɗanyen kaya ne, wanda Amurkan za ta sarrafa su su zama kayayyakin amfani, sannan ta dawo mana da su mu saya da ɗan karan tsada, AGOA ba yarjejeniyar kasuwanci ta ba ni gishiri in ba ka manda ba ce," Wanyonyi a ƙara.
Abin ladabtarwa
Uganda ta yi Allah wadai da matakin da Amurka ta ɗauka na cire ta daga cikin yarjejeniyar AGOA, tana cewa, an yi hakan ne don a ladaftar da ita a kan dokar haramta luwaɗi da ta yi a watan Mayun wannan shekarar, tana nuni da wasiƙar da shugaban kasa Joe Biden ya aika wa Majalisar Dokokin Amurka a kan Uganda.
Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni ya mayar da martani, yana gaya wa mutanensa da kar su damu sosai game da cire ƙasar daga yarjejeniyar. "Wannan matsin lambar daga waje na raini ne - da ake yi wa Afrika kuma dole a ƙi amincewa da shi."
Banda ƴaƴan vanilla, Uganda tana fitar da coffee, da auduga da kuma yadi zuwa Amurka a ƙarƙashin yarjejeniyar kasuwancin.
In ji wasu alƙaluman Amurka, ƙasar ta shigo da kayayyakin Uganda na kimanin dala Miliyan 174 a ƙarƙashin AGOA a shekarar 2022, yayin da ita kuma ta kai kaya na kimanin dala Miliyan $167 zuwa ƙasar ta Afrika.
"Haramcin na Amurka zai cutar da tattalin arziƙinmu saboda kasuwa sunanta kasuwa," Jane Nalunga ƙwararriya a cibiyar Kasuwanci Ta Haɗin-Gwiwa Tsakanin Yankun Kudanci Da Gabashin Afrika ta SEATINI ta gaya wa TRT Afrika. "Muna buƙatar duk manyan kasuwanni domin sayar da hajojinmu".
Saƙo Zuwa Ga Afrika
Odrek Rwabwogo, mai bai wa shugaban ƙasa Museveni shawara na musamman, ya ce matakin na Amurka ya aika wani saƙo ga ɗaukacin al'ummar Uganda - da ma Afrika gaba ɗayanta - cewa yiwuwar bunƙasar tattalin arziƙinsu ya dogara ne da ko sun amince da ra'ayin ko ma wane ne ke riƙe da madafun iko a Amurka."
"Su (ƴan Afrika) ba za su amince da wannan ba. Kuma bai kamata su amincen ba.
Rwabwogo ya ce, yarjejeniyar ta AGOA waɗanda suka ƙirƙire ta sun ƙulla ta ne a matsayin wata manufa ta karamci da hangen nesa da za ta ƙulla dangantaka ta ƙawance da mutuntawa. Amma yanzu, ana amfani da ita a matsayin sandar da ake dukan ƴan Afrika da ita" ya gaya wa TRT Afrika.
Haramcin kasuwancin ya biyo bayan matakin da Bankin Duniya ya ɗauka ne a watan Agusta, na dakatar da bai wa Uganda kuɗaɗe saboda sabuwar dokar haramta luwaɗi, wacce bisa manufa, ta saɓa wa ra'ayin Bankin Duniyar".
A shekarar 2017, shugabannin kasashen Rwanda da Burundi, da Kenya, da Tanzania da kuma Uganda sun yanke shawarar dakatar da shigo da gwanjo da takalma ƴan kwatano daga Amurka domin tallafa wa masana'antunsu na cikin gida. Amurka ta ce hakan ya saɓa wa yarjejeniyar cin gajiya ta AGOA sannan ta dakatar da Rwanda daga yarjejeniyar na tsawon kwanaki 60 a shekarar 2018.
A shekarar 2022, Amurka ta cire Mali, da Habasha da kuma Guinea daga shirin kasuwanci na AGOA. An dakatar da Habasha saboda rikicin cikin gida sannan sauran biyun kuma saboda sauya gwamnati ta hanyar da ta saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa.
Jamhuriyar Tsakiyar Afirka, da Gabon da kuma Nijar, ba za su sake yin kasuwanci da Amurka a ƙarƙashin tsarin kasuwanci mara shinge daga watan Janairu mai zuwa ba, inda Washington ke zargin su da ƙin cika ƙa'idojin yarjejeniyar.
Sake Salon Kasuwanci
Yanzu Afrika tana sake mayar da hankalinta a kan yarjejeniyoyin gudanar da kasuwanci tsakanin ƙasashenta, inda ƙasashe 54 suka muhimmantar da da yin kasuwanci tsakanin junansu. Yarjejeniyar Kasuwanci Mara Shige Ta Ƙasashen Afrika (ACFTA) na da hadafin kawar da shigen kasuwanci, da bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashen Afrika da kuma mayar da hankali kan samar da kayayyakin masu inganci a faɗin nahiyar.
Ƙasashe Arba'in da Huɗu sun amince da yarjejeniyar ta ACFTA, wacce ke da hadafin wanzar da tsarin kasuwanci na babu cuta babu cutarwa da ƙasashen yamma.
"Nahiyar ta samu cigaba wajen bunƙasa kasuwar cikin gida, sakamakon haka ta kafa ƙa'idojin dunƙulewar manufofin tattalin arziƙi," Sakataren gudanarwa na ACFTA ya gaya wa taron AGOA na 2023 kwanan nan.
"Hakan na nufin ya dace mu sauya tunani daga AGOA zuwa ACFTA."
Shugaban ƙasa Cyrill Ramaphosa na Afrika ta Kudu ya dunƙule zancen waje guda a wajen taron, "Lokaci ya wuce da ake kallon Afrika a matsayin wajen da ake samun duwatsu, da ƙasa da turɓaya kawai... Yanzu muna son samun cikakkiyar gajiyar kayanmu."