Harkar adana bayanai ta fi taɓarɓarewa a aikin gwamnati saboda zargin cin hanci da rashawa, a cewar Mista Labaran./ Hoto: TRT Afrika

Daga Umar Yunus, Jos

Adana bayanai al'amari ne mai muhimmanci da ke kai wa ga biyan buƙata a matakai daban-daban na rayuwar ɗan'adam.

Wannan daɗaɗɗiyar al'ada tana daidaita al'amuran ma'abotanta a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Bayanan da ya kamata a ce an adana su, za su iya kasancewa rubutattu ko a cikin hoto, ko bidiyo ko kuma murya.

A tsawon lokaci, mutane sun saba amfani da wannan hanya domin kai wa ga wata buƙata tasu ba tare da fuskantar tangarɗa ba. To sai dai, a ƙasashe masu tasowa irin Nijeriya, adana bayanai na gamuwa da tarnaƙi a matakai daban-daban, abin da ke sa a gaza samun bayanai wadatattu kuma ingantattu.

Wannan al'amari yana taka muhimmiyar rawa wajen kawo koma-baya ga ci-gaban ƙasa, domin yana shafar fannonin rayuwa daban-daban.

Dabarun adana bayanai da ɗan'adam

Wuraren da wannan al'amari ya fi shafa sun haɗa da cikin gida ko a tsakanin iyali da manyan makarantu da ƙanana da asibitoci da kuma harkoki na kasuwanci har ma da hukumomi da kamfanoni da kotuna da dai duk wasu kafofi da cibiyoyi da ke ajiye bayanan al'umma da za a iya neman bayani daga wajensu a kowane lokaci.

A matakin gida ko iyali, wanda shi ne matakin farko na koyon dabarun zaman duniya ga ɗan'adam, ana iya tambayar iyaye wasu bayanai masu muhimmanci game da ƴaƴansu, kamar takardar haihuwa, ko katin asibiti ko sakamakon jarrabawar makaranta, amma su gaza samar da su, saboda ba su san inda suka yasar da su ba.

Wasu iyayen suna da sakaci da rashin daukar abu da muhimmanci, a cewar Mista Seth Labaran jami'in  hukumar Koken Ma'aikata a Nijeriya Public Complain Commission/ Hoto: TRT Afirka 

Wannan babbar gazawa ce, a cewar Mista Seth Labaran, Jami'in Gudanarwar na Hukumar Koken Jama'a, wato Public Complain Commission a wata hira da ya yi da TRT Afrika.

"Wasu iyayen suna da sakaci da rashin daukar abu da muhimmanci wanda ya zame musu jiki; har ta kai ga ba su ɗauki adana bayanai da suka shafe su ko ƴaƴansu da muhimmanci ba," in ji shi.

Bincike

Wasu iyayen jahilci ne yake hana su ba wa muhimman bayanansu kulawar da ta dace. Alal misali, wanda bai iya rubutu da karatu ba, mawuyaci ne ya iya tantance takarda mai ɗauke da muhimman bayanai da wacce ba ta da bambanci da shara, ballantana ya adana ta. A wajen irin waɗannan mutanen, babu wani bambanci tsakanin muhimmiyar takarda da takardar tsire," in ji Mista Seth Labaran.

So tari, rashin adana bayanai, na kawo tarnaƙi ga harkar bincike. Masu bincike a fannonin ilimi daban daban, kan gamu da ƙalubale, yayin da bincikensu ya isa wata gaɓar da ke buƙatar ƙarin bayani daga wata kafar.

Mr Labaran ya ce, hatta manoma da ƴan kasuwa, za su fa'idantu sosai, da suna adana bayanai da suka danganci harkokinsu.

"Manoma sun dogara ne da binciken masana wajen inganta harkar noma. Da za su dinga adana nasu bayanan game da abin da suke aiwatarwa a gonakinsu, da sai sun fi samun sauƙin wajen inganta aikin noma.

Haka kuma, su ma ƴan kasuwa, da za su dinga adana bayanai game da harkokinsu, da sai sun fi samun sauƙin cin gajiyar wani shirin tallafi na gwamnati ko samun rance ko wata garaɓasa daga wajen banki ko kamfani," a cewarsa.

A makarantu, musamman na Firamare da sakandare, ana yawan cin karo da matsalar adana bayanai. Akan samu makarantun da hatta rigistar ɗalibai (school register) babu, ballantana kundin da ya ƙunshi alƙaluman sakamakon jarabawar ɗalibai na kowane zangon karatu (Dossier).

A hirarsa da TRT AFRIKA, Malami Abdullahi Salihu, Shugaban Ƙungiyar Masu Makarantu Masu Zaman Kansu a Ƙaramar Hukumar Jos Ta Arewa ta Jihar Filato, ya ce hakan bai rasa nasaba da hawan ƙawara da ake yi wa harkar ilimi a Najeriya, yana ƙarawa da cewa, harkar ilimi tana daga cikin harkokin da kowa zai iya faɗawa ba tare da samun ƙwarewa ta musamman ba.

"Gaskiya rashin sanin makamar aiki daga ɓangaren masu gudanar da makarantu shi ke jawo irin wannan taɓargazar. A harkar gudanar da makaranta, akwai wasu kundaye da suka ƙunshi bayanan ɗalibai da wajibi ne a adana su, saboda za a iya neman su komai daren daɗewa.

Dakin aije litattefai./ Hoto: TRTAfrika

Abu na uku, shi ne, galibin masu sana'ar koyarwa a wannan zamanin, ba sha'awarsu da sana'ar ba ce ta sa suka shige ta ba, neman mafakar tattalin arziki ta wucin-gadi suke nema kafin su samu wani aikin mai gwaɓi. Ka ga kuwa, babu yadda za a yi irin waɗannan mutanen su jiɓabci al'amarin makarantar yadda ya kamata", a cewar Malamin.

Masani a kan harkar ilimin, ya ƙara da cewa, Ƙyuya da ganda su ma sukan taka muhimmiyar rawa wajen hana wanda aka ɗora wa alhakin kula da adana bayanai yin aikinsa yadda ya kamata.

A asibitoci ma, ana samun matsalar adana bayanan marasa lafiya, inda ''wani lokacin, sai dai mara lafiya ya sake sayen sabon kati kafin ya ga likita.'' a cewar wata ma'aikaciyar asibiti, Salma Muhammad Musa.

Ta kara da cewa ''laifin galibin marasa lafiyar ne, ba na asibiti ba. Salma ta bayyana cewa, a yawancin lokaci, mara lafiya ba ya zuwa asibitin da ƙaramin katin da ke ɗauke da bayanan da za a yi amfani da su wajen nemo katin bayanansa na asibitin wato (hand card).

"Wasu mantawa da katin a gida suke yi yayin da wasu ke ɓatar da nasu, saboda rashin ba shi muhimmancin da ya cancance shi. Duk da cewa mu kan yi amfani da wasu bayanai na daban da muke adanawa, don binciko katin mara lafiyar, amma hakan na ci mana tuwo a kwarya matuƙa.'' in ji ta.

Kazalika, ''salwantar da ƙaramin katin, ba ƙaramar illa yake wa shi kansa mara lafiyar ba; domin kasancewa katin na ɗauke da illahirin bayanai ganin likita da mara lafiya ya yi a baya, duk lokacin da ya zo asibiti da buƙata ta gaggawa ba zai samu ba, saboda sai an ɗauki lokaci ana nemo katinsa.'' a cewar Salma.

Sakaci da cin hanci da rashawa daga Jami'an Gwamnati

Harkar adana bayanai ta fi taɓarɓarewa a aikin gwamnatin saboda cin hanci da rashawa, a cewar Mista Labaran. "Sanannen abu ne, wasu jami'an gwamnati, kan ɓoye kundin bayanai na mutane a ma'aikatu da gangan, da zimmar sai an ba su toshiyar baki kafin su fitar da shi. Wani lokaci kuma, sakaci da halin ko-in-kula da kuma ƙyuya na wasu ma'aikatan ne ke yin sanadiyar ɓatan kundayen bayanan jama'a," in ji shi.

Amma abin lura a nan shi ne, sannu a hankali, fasahar zamani, tana kawar da hanyar adana bayanai da aka sani, tana maye ta da tsarin adana bayanai ta na'ura mai ƙwaƙwalwa.

Ya ci gaba da cewa, tsautsayi kamar gobara ko ambaliya ba su cika ritsa wa da bayanan da aka adana a na'ura mai ƙwaƙwalwa ba, muddin an adana su yadda ya kamata, saɓanin waɗanda ake gani ido da ido.

Fasahar zamani

Sannan kuma, sunan da aka adana bayanan da shi kawai za a rubuta, sai a gano shi cikin sauƙi, ba sai an je ga jidalin ɗage ɗage da kauce kaucen takardu ba. Ga shi kuma adadin bayanan da na'ura mai ƙwaƙwalwa ke adana wa a lokaci ɗaya, ya zarce na wanda za a adana a takardu nesa ba kusa ba.

"Idan mutum bai yi amfani da dabarun adana bayanai ingantattu ba, kamar sanya gaurayen faswod (password), masu kutse za su iya sace bayanan in ji masanin sadarwa Aliyu Ibrahim . /Hoto: TRTAfirka

Sai dai Aliyu ya ce adana bayanai ta na'ura mai ƙwaƙwalwa na da nasa ƙalubalen.

"Idan mutum bai yi amfani da dabarun adana bayanai ingantattu ba, kamar sanya gaurayen faswod (password), masu kutse za su iya sace bayanan. Hakazalika, Biros (virus) na iya lalata bayanan, musamman idan a ka yi sakaci ba a saka manhajar Antibiros (Anti Virus) ba.

A wasu wuraren, kamar ƙauyuka, rashin wutar lantarki, da tsadar saye da kuma kula da na'ura mai ƙwaƙwalwa da rashin cikakken ilimin da ƙwarewar sarrafa ta, kan iya zama tarnaƙi ga tsarin adana bayanai na zamani," Aliyu ya kammala.

A cewar Mista Labaran, mafita ita ce, iyaye su zama masu tsari da tattala duk wasu bayanai da suka shafe su ko ƴaƴansu saboda ƴaƴansu su yi koyi da su. Domin Ƴan'magana na cewa, "Barewa ba ta gudu ɗanta ya yi rarrafe".

Abu na biyu, in ji shi, shi ne, a dinga ɗaukan mataki, gwargwadon yadda doka ta tanada,a kan duk mahalukin da ya yi sakaci,ko ganganci ko ha'incin wajen adana bayanai.

Na uku, a dinga ɗaukan ma'aikata aiki bisa cancanta kuma a horas da su akai akai, don su san makamar aiki yadda ya kamata. Sannan duk wanda ke da alhakin sa ido a kan wani jami'i to ya yi aikinsa tsakaninsa da Allah.

Daga ƙarshe in ji Mista Labaran, dole a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen dagewa a yaƙi ɗabi'ar cin hanci da rashawa; idan ba haka ba kuma, ba za a taɓa ganin yadda a ke so ba.

Tanadin Shari'a game da adana bayanai

Barrister Buhari Ibrahim Shehu, lauya mai zaman kansa ne a Jos, yayin hira da TRT AFRIKA ya ce akwai doka da majalisar ƙasa ta kafa a 2011 da ke tilasta wa hukumomin gwamnati da jami'ansu samar wa ƴan ƙasa bayanai a duk lokacin da suka nuna suna buƙata.

Majalisar dokokin Nijeriy ta kafa doka a 2011 da ke tilasta wa hukumomin gwamnati da jami'ansu samar wa ƴan ƙasa bayanai a duk lokacin da suka nuna suna buƙata. / Hoto: Reuters

"Ita dokar ana kiran ta Dokar Ƴancin Samar Da Bayanai (FOA) wacce a sassanta daban daban ta tanadi cewa ɗan Najeriya na da ƴancin neman bayanai a kowane lokaci, kuma a ba shi, ba tare da wata tangarɗa ba. Sannan ta tanadi hukuncin tara ko ɗauri a kan hukuma ko jami'inta da suka ƙi yi wa dokar biyayya," a cewarsa.

Sai dai, in ji Barrister Buhari, dokar ta bai wa jami'an gwamnati kariya daga tsangwama ko ladaftarwa sakamakon bayar da bayanan.

"Kafin a kafa dokar, jami'an gwamnati kan ja ƙafa wajen miƙa bayanai kan hukumarsu ga mai buƙata, saboda tsoron abin da ka iya biyo baya, wanda galibi kan kai wa ga su samu koma-baya ko ma su rasa aikin ɗungurungun. Amma yanzu dokar ta ba su madogara," ya jaddada.

Lauyan, har wa yau, ya ja hankalin cibiyoyi masu zaman kansu, da ma mutane ɗaiɗaiku game da muhimmancin adana bayanai da kuma hatsarin da ke tattare da yin sakaci da su, yana cewa, rashin adanawa da kuma rashin yin taka-tsan-tsan da bayanai, kan sa mutum ya rasa wata muhimmiyar dama a rayuwa, ko rasa lafiya ko ma rai gabaɗaya.

TRT Afrika