Gomman mutane ne suka mutu yayin da daruruwa suka jikkata cikin ‘yan kwanaki da barkewar rikici a Sudan, tsakanin gwamnatin mulkin sojin kasar da dakarun rundunar tsaro ta Rapid Support Forces da aka fi sani da RSF.
Duk da cewa bangarorin biyu sun amince da tsagaita wuta a ranar Lahadi, sai da sabon rikici ya barke tsakanin sojojin bangarorin biyu.
Da ma an tsagaita wutar ne don a samu damar kai "agajin gaggawa" da kuma fitar da mutane daga yankunan da lamarin ya shafa.
Tun da farko shugaban kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan da Janar Mohamed Hamdan Dagalo na RSF sun amince da tayin Majalisar Dinkin Duniya na tsagaita wuta daga karfe hudu zuwa karfe bakwai na yamma a agogon kasar, kuma sun amince da wannan tsari.
Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Sudan din na daga cikin mutum biyun da ke daukar hankali a wannan rikici. To wane ne Janar Abdel Fattah al Burhan?
Duk da cewa al-Burhan bai fara yin suna ba sai a shekarar 2019, ya dade yana jan zarensa tare da taka rawa a rundunar sojin kasar, inda aka tura shi aiki a yankin Darfur tun farkon shekarun 2000 lokacin da ake rikici a can, inda ya dinga samun karin girma har ya zama kwamandan yanki a 2008.
Kuma a lokacin da Kotun Duniya ta ICC ta dinga tuhumar tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir da sauran manyan jami’an gwamnatin Sudan da laifin kisan kare dangi da cusguna wa mutane kan abin da ya faru a Darfur, al-Burhan da abokinsa a wancan lokacin kuma abokin hamayyarsa a yanzu, Mohamed Hamdan “Hemedti” Dagalo ba su fuskanci tuhuma ba.
An shafe shekaru al-Burhan yana nesanta kansa daga laifukan da aka aikata a Darfur, inda rundunar soji tare da goyon bayan rundunar RSF, suka murkushe wani tawaye a rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutum 300,000 tare da raba wasu miliyan 2.7 da muhallansu.
Al-Burhan a takaice
- An haifi Abdel Fattah al-Burhan a watan Yulin 1960 a kauyen Gandatu da ke arewacin Sudan
- Ya yi karatunsa na firamare da sakandaire a kauyensu
- Daga baya ya koma garin Shendi don kammala karatunsa kafin ya shiga kwalejin sojoji
- Bayan kammala kwalejin soji, al-Burhan ya yi aiki a birnin Khartoum a cikin rundunar sojin Sudan
- Yana gaba-gaba a yakin Darfur da aka yi
- Sannan da shi aka yi Yakin Basasar Sudan na biyu a Sudan ta Kudu da kuma sauran yankunan kasar.
Samun horo da kwarewa
A shekarar 2018, al-Burhan ya samu karin girma zuwa babban hafsan rundunar sojin Sudan, a 2019 kuma ya je wasu kasashe irin su Jordan da Masar don kara samun horon soji.
Burhan yana kan mukamin babban sufeto na rundunar sojin Sudan, wato na uku mafi girma a cikin manyan janar din sojin kasar, a lokacin da aka yi juyin juya halin da ya tumbuke al-Bashir daga mulki a watan Afrilun 2019.
Janar Burhan ya kasance na kut da kut ga Shugaba al-Bashir, amma da aka hambarar da Omar al-Bashir sai ministansa na tsaro Laftanal Janar Awad Mohamed Ahmed Ibn Auf ya maye gurbinsa, inda masu zanga-zanga suka sake tilasta masa yin murabus.
Da Janar Ibn Auf ya sauka, sai Janar al-Burhan ya maye gurbinsa, inda ya zama shugaba mafi karfin iko a kasar a yanayi na kokarin mika mulki, ya kuma zama mai tsanani da samun karfin iko a Sudan.
An nada al-Burhan a matsayin shugaban kwamitin mika mulki na rundunar soji TMC bayan hambarar da Shugaba al-Bashir da aka yi.
Bayan watanni kadan sai matsin lambar kasashen duniya ta sa aka cimma yarjejeniyar raba iko a 2019 tare da samar da wani kwamitin hadin gwiwa na soji da farar hula da zai maye gurbin TMC, wanda zai tabbatar an gudanar da zabuka a kasar a wannan shekarar.
An nada Janar Burhan a matsayin shugaban wannan kwamitin. Amma da lokacin mika mulki ga farar hula ya karato a karshen 2021, sai Janar Burhan ya nuna alamun ba ya son mika mulkin.
Janar Burhan ya kulla kawance tare da samun kusanci da kasashe irin su Hadaddiyar Daukar Larabawa da Masar da Saudiyya, wadanda suka dinga goyon bayansa shi da shugaban rundunar RSF Hemedti a kokarinsu na tumbuke al-Bashir.
Sannan alakar al-Burhan da Masar ta sa bangrorin biyu sun dinga gudanar da atisayen soji tare kuma shi kansa al-Burhan ya samu horo a rundunar sojin Masar.
Dangantaka tsakanin rundunar sojin da ta RSF ta yi tsami sosai inda dukkan bangarorin ke kwadayin mulki, kuma wannan rikicin da ake yi a yanzu manuniya ce dake bayyana lalacewar dangantakar tasu.
A wata yarjejeniya da aka cimma a watan Disamban bara tsakanin rundunar sojin kasar da RSF da kuma dakarun da ke goyon bayan mulkin farar hula, rundunar sojin ta amince za ta koma bariki tare da sanya RSF a karkashinta.
Sai dai ga alama dukkan yarjeniyoyin ba lallai su yi tasiri ba a yanayin da ake ciki.