Ministan Kula da Harkokin Babban Birnin Kampala na Uganda ya gode wa Turkiyya bisa goyon bayan ajandarsu ta ci gaban ƙasar tare da yin alkawarin ƙarfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Hajjat Minsa Kabanda ta faɗi hakan ne a ranar Talata a Kampala, inda aka yaba wa kodinetan Hukumar Hadin Kan Kasa da Kasa ta Turkiyya (TIKA) a Uganda, Omer Aykon a matsayin wakili nagari ga hukumar bayar da agaji ta gwamnatin Turkiyya.
Kabanda ta ce, a lokuta da dama, Turkiyya ta tabbatar da ƙawancenta da kasar Uganda, inda ya kuma gode wa TIKA bisa yadda take ba da tallafi mai muhimmanci ga dimbin ayyukan Uganda a fannoni daban-daban da suka hada da noma da ilimi, da kiwon lafiya.
Ta bayyana muhimmancin ci gaba da hadin gwiwa don inganta ci gaban tattalin arziki da ci gaban zamantakewa a Uganda tare da tallafa wa ci gaban marasa galihu.
'Ci gaba mai ɗorewa'
"Ina fatan wannan hadin gwiwar za ta ci gaba da samun damar ci gaba mai ɗorewa," in ji ta.
Aykon ya nanata ƙudurin Turkiyya na tallafa wa ajandar ci gaban Uganda.
"Za mu ci gaba da bayar da taimakon raya kasa ga abokanmu domin rage radadin talauci da kawo sauyi," in ji shi.
Ya zuwa yanzu hukumar ba da agaji ta Turkiyya ta gudanar da ayyuka 75 a kasar Uganda kadai tare da fadada ayyukanta a ayyukan hadin gwiwa daban-daban a kasashe 170 ta hanyar ofisoshinta na gudanar da shirye-shirye guda 62 da ke cikin kasashe 60 na nahiyoyi biyar, a cewar Aykon.