Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya bai wa jami'an tsaron ƙasar umarni su "gaggauta" kuɓutar da mutanen da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihohin Borno da Kaduna da ke arewacin ƙasar.
Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, kwana guda bayan wasu ƴan bindiga sun shiga wata makarantar sakandare a jihar Kaduna inda suka yin awon gaba da ɗalibai kusan 300. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun ranar Alhamis.
Kazalika ranar Laraba wasu ƴan bindigar sun sace gomman mutane, galibinsu mata da ƙananan yara ƴan gudun hijira a Gamboru Ngala yayin da suka je daji domin saro itacen girki.
A sanarwar da ya fitar ranar Juma'a, Shugaba Tinubu ya nuna baƙin cikinsa game da garkuwar da aka yi da mutanen, sannan ya sha alwashin kuɓutar da su.
"Na samu bayanai daga manyan jami'an tsaro game da hare-hare biyu da aka kai a Borno and Kaduna, kuma ina da ƙwarin gwiwar cewa za a kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su," in ji Shugaba Tinubu.
Ya ƙara da cewa, "Na umarci jami'an tsaro da na leƙen asiri su gaggauta kuɓutar da waɗanda aka sace sannan su tabbatar da hukunta waɗanda suka aikata wannan ɗanyen-aiki."
Shugaba Bola Tinubu ya jajanta wa iyalai da ƴan'uwan mutanen da aka yi garkuwa da su a jihohin biyu sannan ya ce nan ba da jimawa za a kuɓutar da dangin nasu.