Shugaba Tinubu ya ce dole ne kasashen yankin Tafkin Chadi su yi garambawul a tsarin bai wa jami'an tsaro horo idan suna so su murkushe 'yan ta'adda./Hoto: Shafin Facebook na Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi kira ga kasashen yankin Tafkin Chadi su sauya tsarin bai wa sojojinsu horo domin dakile hare-haren ta'addanci da ke faruwa a yankin.

Ya yi kira ne ranar Juma'a a Kaduna yayin da ya halarci bikin yaye sojoji a makarantar horar da dakarun tsaro ta Jaji.

Shugaba Tinubu ya ce ya zama dole a sauya fasalin horar da sojojin domin kasashen yankin suna yaki ne da "masu kai hare-hare da ke yawan sauya wurin zama kuma wadanda ba su da tabbas" sannan ba sa yin biyayya ga dokokin yaki.

Ya yi kira ga kasashen Afirka su yi aiki tare domin tunkarar makiyansu, yana jinjina wa rundunar tsaron hadin-gwiwa ta yankin Tafkin Chadi ta kasashen Nijeriya, Kamaru, Nijar da Chadi bisa aikin da take yi na tabbatar da tsaro a yankin.

''Dole mu zage dantse wurin sauya tsarin horar da sojoji. Mutanen da muke yaki da su ba kamar sojoji ba ne da ke da tsarin yaki, a'a, muna fama da masu kai hare-hare da ke yawan sauya wurin zama kuma wadanda ba su da tabbas

''Dole mu yi garambawul domin murkushe wannan bala'i. Hakan yana bukatar sauya tunani da kayan aiki," in ji Shugaba Tinubu.

Nijeriya dai tana fama da hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa musamman a arewa maso gabas da arewa maso yammacin kasar.

Bayanai sun nuna cewa hare-haren wadannan kungiyoyi sun yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.

TRT Afrika