Shugaban Nijar Janar Abdourahamane Tiani, ya kai ziyararsa ta farko ga wata runduna ta dakarun tsaron ƙasar da ke yaƙar ‘yan ta’adda a jihar Tillaberi.
Janar Tiani ya kai ziyarar ne domin ƙarfafa wa dakarun gwiwa kuma yi wa waɗanda harin ta’addanci na watan Disamban shekarar 2024 ya shafa jaje.
Rahotanni sun ce shugaban da ya tafi sansanin sojojin ta jirgi mai sauƙar angulu tare da manyan sojoji ya kuma ziyarci kamfanin Société des Mines du Liptako mai haƙar zinare.
Yayin ziyarar kamfanin, Janar Tiani ya jaddada jajircewar gwamnatin ƙasar wajen farfaɗo da tattalin arziƙinta tare da tsaron yankin.
Shugaban wanda ya sami rakiyar ministan tsaro, Lutanan Janar Salifou Mody da babban hafsan sojojin ƙasan Nijar, Birgediya Janar Moussa Saloua Barmou, da kuma shugaban ma’aikatan shugaban ƙasar, Kanar Ibro Amadou, ya fara ziyararsa ne da barikin sojoji na Samira.
Kuma daga bisani ya ziyarci sansanin sojin da ke Libiri, kilomita kaɗan daga kan iyakar ƙasar da Burkina Faso inda aka yi masa cikakken bayanai game da tsarin tsaron da ake da shi tare da nuna ƙoƙarin da ake yi na kare yankin mai muhimmanci.