Tattaunawar zaman lafiya a Sudan ta Kudu na fuskantar barazana a yayin da zaɓe ke ƙaratowa

Tattaunawar zaman lafiya a Sudan ta Kudu na fuskantar barazana a yayin da zaɓe ke ƙaratowa

Kenya na ta karbar bakuncin tattaunawar manyan jami'ai tun watan Mayu tsakanin wakilan gwamnati da na 'yan tawaye masu adawa.
Duk da yarjejeniyar, ana yawan samun barkewar rikici a kasar mai mutane miliyan tara. / Photo: Reuters

Tattaunawar zaman lafiyar Sudan ta Kudu da aka kusa kammalawa na fuskantar barazana yayin da 'yan adawa ke bukatar a soke wata doka da ta bayar da damar a kama mutane a ɗaure su ba tare da umarnin kotu ba, domin sanya hannu kan ƙudirin yarjejeniyar.

Kenya na ta karbar bakuncin tattaunawar manyan jami'ai tun watan Mayu tsakanin wakilan gwamnati da na 'yan tawaye masu adawa da ba sa cikin waɗanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar 2018 da ta karkare da yaƙin basasar da ya yi ajalin mutum 400,000 tare a raba miliyoyi da matsugunansu.

Duk da yarjejeniyar, ana yawan samun barkewar rikici a kasar mai mutane miliyan tara.

Pagan Amum Okiech, wanda ke wakiltar banraen 'yan dawar Sudan ta Kudu a wajen tattaunawar ya shaida wa AP a daren Talata cewa zai zama "Shirme kenan a sanya hannu kan yarjejeniyar matukar Shugaban Ƙasa ya sanya hannu kan tsattsaurar Dokar Tsaron Kasa."

Babban zaɓe a karo na farko

A makon da ya gabata, majalisar dokoki ta amince da ƙudurin dokar 2015, kuma Shugaban Kasa Salva Kiir na da wa'adin kwanaki 30 na sanya hannu kafin ta zama doka. Wannan na zuwa ne a yayinda kasar za ta gudanar zabe a karon farko a ranar 22 ga Disamba.

"Wannan doka ta saba wa ginshikan hakkoki da 'yancin 'yan Sudan ta kudu, tana kawar da bigiren farar hula da siyasa," in ji Amum. "Babu wani digon dimokuradiyya a wannan doka."

Daga masu halrtar tattaunawar har da Kungiyar Tallafawa Al'umma, wata kungiya da ba ta neman riba ba da ke amfani da daliban jami'a da wadanda suka kammala karatunsu. Edmund Yakani ya soki dokar ta tsaro inda ya ce ta "kirkiri mummunan ynyi ga tattaunawar."

Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Human Rights Watch ma ta yi kira ga kiir da ya yi watsi da dokar mai rikita-rikita, tana mai cewar za ta sake dagula batun kare hakkokin dan adam da bayar da karin karfi ga hukumomin tsaron kasa da suke da tarihin keta hakkokin dan adam.

'Tattaunawar fata nagari'

Tattaunawar da aka bai wa sunan - Tumaini, ma'ana fata nagari a harshen Swahili - ta samar da daftarin yarjejeniyar da ke neman ƙara wa'adin gwamnatin riƙo tare da ɗage lokacin zaɓen da ke tafe, domin samun damar kammala rubuta kundin tsarin mulkin kasar da dokokin zabe.

Sannan a fitar da iyakokin mazabu da hadaddun hukumomin tsaro da aka bayar da shwarar samar da su a tattanawar 2018.

Wasu jakadun Yammacin duniya sun bayar da shawarar dage lokacin zaben "don tabbatar da zabe ingantacce."

Kiir na nan a kan bakansa game da gudanar da zaben a Disamba inda ya ma ya soki shawarar jakadun.

TRT Afrika