Tattalin arzikin Nijeriya ya ƙaru da kaso 3.46 a rubu’i na uku na shekarar 2024 a ma’aunin GDP, kamar yadda Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta sanar.
A wata sanarwa da da ofishin babban mai ƙididdiga na hukumar NBS Prince Adeyemi Adeniran Adedeji ya fitar, ya bayyana cewa an samu ƙarin 0.9 cikin 100 idan aka kwatanta da adadin da aka samu a rubu’i na uku na shekarar 2023 inda aka samu 2.54.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa an samu ƙaruwa da kaso 0.27 cikin 100 a rubu’i na uku na bana idan aka kwatanta da wanda aka samu a rubu’i na biyu na bana wato kaso 3.19 a cikin 100.
Sai dai haɓakar tattalin arzikin Nijeriyar na zuwa ne a daidai lokacin da alƙaluman hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya karu zuwa kashi 33.88 a watan Oktoban 2024, adadin da ya nuna an samu ƙarin kashi 1.18 cikin dari daga kashi 32 cikin 100 da aka samu a watan Satumban 2024.
Sai dai gwamnatin Nijeriya na cewa tana iya bakin ƙoƙarinta wurin rage hauhuwar farashin kayayyakin da haɓaka tattalin arziƙin ƙasar.