Mr Modi ya ce dukkan mambobin G20 sun amince Tarayyar Afirka ta zama sabuwar mamba a kungiyar./ Hoto: AFP

Tarayyar Afirka ta zama sabuwar mamba a kungiyar kasashen G20 masu karfin tattalin arziki ranar Asabar bayan Firaiministan India Narendra Modi ya gayyace ta.

Fadada kungiyar babbar nasara ce ta fannin diflomasiyya ga Modi, wanda zai sake fafatawa azaben kasar a shekara mai zuwa kuma y yi amfani da damar karbar bakuncin taron wajen kara wa kansa kima a idanun duniya.

Kafin ya bude taron, Modi ya gaishe da shugaban Tarayyar Afirka kuma shugaban kasar Comoros Azali Assoumani inda ya rungume shi.

"India ta nemi a bai wa Tarayyar Afirka gurbi na dindindin na zama mamba a kungiyar G20. Na yi amannar cewa kowa ya amince da hakan," a cewar Modi a jawabinsa ga mahalarta taron.

"Ina kira ga shugaban Tarayyar Afirka ya zo ya zauna a kujerarsa ta dindindin a G20 bayan amincewar kowa da kowa," in ji shi, inda ya doka sandar da ke hannunsa wacce ke nuna an yarda da matakin.

Daga nan ne Assoumani ya je ya zauna a wurin da shugabannin kungiyar suka zauna bayan Ministan harkokin wajen India S. Jaishankar ya yi masa iso.

TRT Afrika da abokan hulda