Nijeriya ta soma tattaunawa da bangarori da dama domin yiwuwar shiga kungiyar kasashen G20 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya.
Kakakin shugaban kasar Mr Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a yayin da yake sanar da shirin Shugaba Bola Tinubu na tafiya kasar India ranar Litinin.
Shugaban Indiya Naredra Modi shi ne shugaban G20 a halin da ake ciki. Kazalika Afirka ta Kudu ce kadai mamba a cikin kungiyar daga Afirka.
"Bola Tinubu zai bar Abuja ranar Litinin don halartar taron shugabannin G-20 a New Delhi, India, bisa gayyata ta musamman daga Firaiministan India, Narendra Modi.
A gefen taron, shugaban kasar zai halarci taro kan Nijeria da India da kuma taron kasuwanci tsakanin Nijeriya da India," a cewar Mr Ngelale a sanarwar da aka wallafa a shafukan sada zumunta na gwamnatin Nijeriya.
Ya kara da cewa Shugaba Tinubu zai yi amfani da wannan dama wajen jawo hankalin 'yan kasuwa da kamfanoni na kasashen duniya su kara zuba jari a kasar.
"Duk da cewar akwai bukatar Nijeriya ta zama mamba ta G-20, gwamnati ta soma tattaunawa mai fadi da zummar sanin amfani da hatsarin da ke tattare da zama mamba a kungiyar," in ji kakakin na shugaban kasa.
Ya kara da cewa: "Da zarar an kammala tattaunawa, gwamnati za ta yanke hukunci kan ko ta nemi zama" mamba a kungiyar ko akasin haka.