Tarayyar Afirka (AU) ta bayyana damuwa game da rikice-rikice da ƙwatar mulki ta hanyar da ta saɓa wa kundin tsarin mulki a Afirka.
Babban jami'in Tarayyar Afirka kan harkokin tsaro da zaman lafiya Sarjoh Bah ya bayyana lamarin a matsayin "abin takaici".
Yankin Kahon Afirka, Sahel da gabashin Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo na daga yankunan da ake gwabza rikici a Afirka, Bah ya shaida wa taron tsaro na nahiya a hedikwatar Tarayyar Turai da ke Addis Ababa babban birnin Ethiopia.
Dubban mutane sun rasa rayukansu a yankunan da ake yin rikice-rikicen.
Barazanar da ke tafe
"Duk da ƙaruwar daukar matakai a matakin kasa da kasa don yaki da ta'addanci da tayar da zaune tsaye a yankin Kusurwar Afirka, yankunan Manyan Tafkuna, da Mozambique, na daga cikin wuraren da kalubalen ke ci gaba," in ji Bah a wajen taron Shugabannin Rundunonin Soji da na tsaro na Kungiyar karo na 19 a ranar Talata.
Ya kara da cewa "Dole ne matakan da za mu dauka su tunkari wadannan kalubale da ke bullowa da dabarun 'yan tayar da kayar bayan. Dole ne kuma mu koyi yadda za mu tsara ayyukan tabbatar da tsaro, tare da inganta yanayin hasashen afkuwar wani rikici."
A ranar Litinin, Bah ya bayyana damuwar cewa Afirka na iya shan wahala daga rikicin wata nahiyar da zai tsallako cikinta.
"Duniya a yau na fuskantar rikici a yankuna daban-daban, gogayyar manyan kasashe masu hamayya da juna, da tsarin tafiyar da duniya wargajajje,' in ji Bah.
'Babu garkuwa'
"Afirka ba ta da garkuwa daga wadannan kalubale, a yayin da muke shaida karuwar tsaro a kasashe wanda ke jarabtar zaren da ya kulle tsarin tsaronmu."
Makarantar Nazarin Dokokin Jinkai ta Geneva ta bayyana cewa a yau a Afirka akwai rikice-rikicen 'yan bindiga har guda 35.