Bashin da ake bin Nijar ya karu zuwa CFA biliyan 187.136 kwatankwancin dala miliyan 304 / Hoto:AFP 

Hukumar da ke kula da basussuka ta yankin yammacin Afirka ta bayyana cewa takunkuman da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS da kungiyar hada-hadar kudaden ta yammacin Afirka suka kakaba wa Nijar sun taka rawa wajen hana kasar biyan basussukan da ake bin ta.

Bashin da ake bin Nijar ya karu zuwa Cfa biliyan 187.136 kwatankwancin dala miliyan 304 tun daga wata Yulin 2023 sakamakon yanayin juyin mullki da kuma matakin dakatar da ita daga kasuwannin hada-hadar kudaden Yammacin Afirka.

Hukumar kungiyar kasashen da ke amfani da kudaden Cfa ta UMOA Titres ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata,

Ta kara da cewa har yanzu Nijar ba ta biya bashin da ake bin ta na kudin ruwa kusan Cfa biliyan 2.464 ($4 m) ba.

''Wannan lamari na bashin kudin ya biyo bayan takunkumin da taron shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar tattalin arziki da hada- hadar kudaden Afirka ta yamma ya kakaba wa kasar Nijar," in ji hukumar.

ECOWAS da kungiyar hada-hadar kudaden yammacin Afirka sun dakatar da Nijar daga kasuwannin hada-hadar kudi na yankin da kuma babban bankin shiyyar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a watan Yuli inda suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum.

Kungiyar ta kakaba wa gwamnatin mulkin sojin Nijar takunkumai masu tsauri ciki har da hana ta amfani da kudaden ajiyar Nijar na kasashen ketare da ke bankin shiyyar tare da barazanar yin amfani da karfin soji domin maido da tsarin mulkin dimokuradiyya a kasar.

Reuters