Dakarun da ke goyon bayan Janar Al-Burhan da na tsohon mataimakinsa Janar Dagalo sun soma yaki da juna tun watan Afrilu./Hoto:AFP

Gwamnatin Sudan ta bai wa ma’aikatan diflomasiyyar Chadi wa’adin awa 72 su fita daga kasar a wani mataki na tabarbarewar hulda tsakanin kasashen biyu.

Kafar watsa labaran kasar ce ta bayyana haka ranar Lahadi.

Ta ambato hukumomin Sudan suna cewa jami’an diflomasiyyar na Chadi sun rasa martaba ta ci gaba da zama a Khartoum, don haka dole su tattara kayansu su fita daga kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Sai dai ba a bayyana sunaye da mukaman jami'an diflomasiyyar da aka kora daga Sudan ba.

A nata bangaren, Chadi ta kori ma'aikatan diflomasiyyar Sudan da suka hada da babban jami'in diflomasiyya a ofishin jakadancin Sudan da ke Chadi, da babban jami'in tsaron ofishin da kuma ma'aikata biyu, kamar yadda gwamnatin Chadi ta bayyana ranar Asabar.

An dauki matakin ne bayan wani babban jami'in sojin Sudan Janar Yassir al-Attaya ya yi "kalamai masu nauyi marasa dalili," sannan shi ma ministan harkokin wajen Sudan ya maimaita su a wani gidan talbijin, in ji sanarwar da kakakin gwamnatin Chadi ya fitar.

"Wadannan kalamai da jami'in gwamnatin Sudan suka yi a kan Chadi da gwamnatin kasarmu ba abu ne da za mu amince da shi ba , kuma suna tunzura jama'a sannan cike suke da wata kullalliya," a cewar sanarwar.

Yaki ya barke a Sudan tun watan Afrilu tsakanin dakarun sojin kasar da na rundunar Rapid Support Forces (RSF) lamarin da ya yi sanadin kisan dubban mutane, sannan miliyoyi suka tsere daga gidajensu, ciki har da dubbai da suka tsallaka cikin Chadi.

TRT Afrika da abokan hulda