Sojojin Sudan sun ƙwace garin Soba da ke gabashin babban birnin kasar Khartoum a ranar Litinin a wani sabon cigaba na soji da suka samu kan dakarun Rapid Support Forces (RSF).
Dakarun Sudan Shield Forces, da ke ƙawance da rundunar sojin, sun ce dakarunsu sun ƙwace iko da yankin.
Kungiyar ta fitar da wani bidiyo da ke nuna kwamandanta Abu Agla Keikel a cikin ofishin 'yan sanda a garin.
Keikel ya fice daga RSF a watan Oktoba 2024.
Akwai yiwuwar a taƙaita tasiri RSF
Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa dakarunta sun ƙwace babbar gadar Soba da ke kan Kogin Blue Nile da kuma garin Soba bayan arangama da mayakan na RSF.
Masu fafutuka a shafukan sada zumunta sun wallafa bidiyoyi da dama na sojojin da ke kan gadar a karon farko tun bayan barkewar fadan a watan Afrilun 2023.
Kame yankin gadar zai takaita zirga-zirgar dakarun RSF a yankunan Gabashin Nilu, inda gadar al-Manshiya ta kan kogin Blue Nile ba ta saura da komai ba sai tsirarun bangarorin 'yan tawaye na RSF.
Wannan gada ta hade yankin Gabashin Nilu da yankunan gabashin birnin Khartoum.
Sojojin Sudan sun kuma ƙara kutsawa zuwa yammacin kogin Blue Nile zuwa yankin Al-Baqir, wanda ya kasance wata hanyar shiga birnin Khartoum daga jihar Al-Jazirah.
Cigaba da kutsawa
Wannan sabon cigaban ya zo ne yayin da sojojin ke ci gaba da karfafa nasarorin da suka samu na soji a bangarori da dama a birnin Khartoum da yankin Gabashin Nile na birnin Bahri, wata muhimmiyar tunga ta RSF.
A ranar Lahadin da ta gabata ne sojojin kasar Sudan suka ƙwace garin Alkotainh da ke jihar White Nile a kudancin Sudan.
Alkotainh, mai tazarar kilomita 100 kudu da birnin Khartoum, shi ne gari daya tilo da RSF ke iko da shi a kudancin Sudan.
Har yanzu dai kungiyar 'yan ta'addar tana iko da hudu daga cikin jihohi biyar na Darfur, yayin da arewaci da gabashin Sudan ke ci gaba da fama da yakin basasa.
Muhimman wurare
A jihar Khartoum mai kunshe da garuruwa uku, a yanzu sojoji suna rike da kashi 90% na yankin Bahri a arewa, mafi yawan yankin Omdurman a yamma, da kuma kashi 60% na tsakiyar birnin Khartoum, inda Fadar Shugaban Ƙasa da filin jiragen sama na kasa da kasa suke.
Dakarun soji sun kusan kewaye wadannan wurare masu muhimmanci, yayin da mayakan RSF ke ci gaba da zama a cikin unguwanni a gabashi da kudu.
Sojojin Sudan da RSF sun fara gwabza yaki ne tun tsakiyar watan Afrilun 2023 wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 20,000 tare da raba wasu miliyan 14 da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin yankin.
Bincike daga jami'o'in Amurka, ya ƙiyasta cewa adadin wadanda suka mutu ya kai kusan 130,000.
Kiraye-kirayen gamayyar kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya na kara ta'azzara, tare da gargadin wani bala'in jinƙai da ke tafe yayin da miliyoyin mutane ke fuskantar yunwa da mutuwa sakamakon karancin abinci.
Rikicin ya bazu zuwa jihohi 13 daga cikin 18 na kasar Sudan.