Rundunar Sojojin Kasa na Sudan ta kaddamar da hare-hare ta sama na farko a kan wuraren da ke hannun dakarun rundunar Rapid Support Forces (RSF) a fadar shugaban kasar.
RSF na rike da wuraren ne tun watan Afrilu lokacin da fada ya kaure tsakanin bangarorin biyu.
A wancan lokacin RSF ta sanar da cewa dakarunta sun mamaye Hedikwatar Bayar da Umarnin Soji da ke kusa da fadar shugaban kasa.
Hakan na zuwa ne a yayin da Amurka, Norway da Birtaniya suka kara yin kira a yi gaggawar tsagaita wuta a Sudan.
Sojojin Sudan sun yi ta luguden wuta kan yankunan da ke hannun dakarun RSF da ke kusa da Rundunar Sojojin Motoci Masu Sulke a Khartoum babban birnin kasar.
Kazalika sojin na Sudan sun kai hare-hare ta sama a wuraren da ke hannun RSF a Khartoum, Omdurman da Bahri.
Tun da farko rundunar sojin Sudan ta bayar da sanarwar kashe gomman dakarun RSF sannan ta lalata motocinsu na yaki guda 10 a hare-haren da ta kai a rundunarsu ta yaki da ke kudancin Khartoum.
An kwashe sama da kwana 100 ana fafatawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, musamman a wurare masu muhimmanci da ke babban birnin kasar da Yammacin Sudan.
Alkaluma sun nuna cewa yakin ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 3,000 sannan dubbai suka jikata, yayin da sama da mutum miliyan hudu suka yi hijira a cikin kasar da ma kasashen da ke makwabtaka.