An shafe sama da makonni takwas ana rikici tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun RSF. Hoto/AFP

Rundunar sojin Sudan na ta kokarin kare wani gini wanda ake kyautata zaton an ajiye makamai masu yawa a kudancin Khartoum, inda ginin yake kusa da wani defo na ajiye fetur da gas wanda mazauna yankin ke fargabar wurin zai iya bindiga.

Rundunar tsaro ta RSF a mako na takwas na yakin da suke yi da sojojin na Sudan sun kai hari a ginin na Yarmouk da yammacin Talata kafin suka janye bayan musayar wuta mai karfi da suka yi da sojojin kasar, kamar yadda shaidu suka bayyana.

An ci gaba da jin karar harbe-harbe har a safiyar Laraba.

“Tun jiya, an ta musayar wuta inda aka rinka amfani da jiragen sama da makaman atilari a kasa,” kamar yadda Nader Youssef, wani da ke zaune a kusa da Yarmouk ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Sakamakon ginin na kusan defo din fetur da gas, “kowace irin fashewa za ta iya tarwatsa jama’ar da ke yankin baki daya”, in ji shi.

Akasarin abubuwa sun lalace a birnin na Khartoum, inda ake yawan dauke ruwa da wuta, haka kuma sata na karuwa.

Makonni ana yaki mai tsanani

RSF din ta kwace wurare da dama a babban birnin Sudan din bayan soma yakin a ranar 15 ga watan Afrilu.

Hare-hare ta sama da luguden wutar da makaman atilare suka rinka yi ba su nuna wasu alamu na tarwatsa su ba, sai dai idan wannan yakin ya ci gaba, RSF din za ta iya fuskantar matsalar samun makamai da kuma fetur.

Rikici a birane uku na Sudan da suka hada da Khartoum da Bahri da Omdurman ya kara kazanta tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 12 ta kawo karshe a ranar 3 ga watan Yuni bayan an sha saba ta.

Wannan rikicin ya mayar da hannun agogo baya ta fannin mika mulki ga farar hula shekaru hudu bayan wata zanga-zanga ta jawo an hambarar da gwamnatin Omar al Bashir.

Sojojin da RSF wadanda tare suka gudanar da juyin mulki a 2021, sun yi hannun riga kan batun da ake yi na yunkurin mayar da rundunar ta RSF karkashin sojojin Nijeriya duk a shirin mayar da mulkin a hannun farar hula.

Sama da mutum 1,428,000 suka rabu da muhallansu a cikin Sudan haka kuma sama da mutum 476,800 aka kiyasta cewa sun gudu sauran kasashe masu makwaftaka da Sudan din kamar yadda wata kiddiga da kungiyar ‘yan ci rani ta duniya IOM ta wallafa a ranar Talata.

Ma’aikatar lafiya ta Sudan ta dauki alkaluma na akalla mutum 780 da suka rasu sakamakon wannan rikicin. Haka kuma an kashe karin daruruwa a birnin Geneina da ke Yammacin Darfur. Jami’an lafiya sun ce akwai gawarwaki da dama wadanda ba a karba ba ko kuma ba a rubuta su a alkaluma ba.

TRT World