Babban Hafsan Sojojin Saman Nijeriya, Air Marshall Hasan Abubakar, ya nemi a yi bincike kan rahoton da ke cewa jirgin yaƙinsu ya kashe wasu fararen-hula a ƙauyen Zakka da ke ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina a arewa maso yammacin ƙasar.
Rahotanni dai sun ce wasu jerin hare-haren na sojin saman ƙasar sun kashe mutum shida yawanci ‘yan gida ɗaya a ƙauyen Zakka yayin da sojin ke fatattakar ɓarayin daji ranar 15 ga watan Fabrairu.
Wata sanarwar da mai magana da yawun sojin saman ƙasar, Air Vice Marshal, Olushola F Akinboyewa, ya fitar ranar Talata ta ambato Air Marshal Abubakar yana neman a “ɗauki matakan da suka dace” bayan bincike kan gaskiyar rahoton kashe fararen-hular.
Sanarwar ta ce ɓangaren sojin sama na dakarun Operation Fasan Yanma ya ƙaddamar da hare-haren sama da suka yi sanadin kashe ɓarayin daji da dama tare da daƙile harin da suka kai wa ‘yan sandan kwantar da tarzoma da ‘yan sintiri a ƙauyen.
“An ƙaddamar da hare-haren ne bayan an samu bayanai cewa ɓarayi sun kai wa ‘yan sandan kwantar da tarzoma hari inda aka kashe ‘yan sanda biyu da kuma ‘yan sintiri huɗu yayin da ‘yan bindigar da suka kai harin suka ɓuya a tsaunukan Yauni,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce nan-take sojin saman Nijeriya suka far ma ɓarayin dajin a maɓoyarsu.
Bayan hakan ne rundunar sojin saman ta ji labarin cewa hare-haren da ta kai sun rutsa da fararen-hula.
“Duk da cewa wannna iƙirarin da ake yi abin takaici ne, yana da muhimmanci a jaddada cewa iƙirarin zai ci gaba da kasancewa zargi har sai lokacin da aka kammala cikakken bincike,” in ji sanarwar.
Cikin ‘yan watannin bayan nan dai an samu aukuwar hare-haren sama da suka kashe fararen-hula bisa kuskure a jihohin Sokoto da Zamfara.