Sojojin Rasha da wasu jami'ai daga ma'aikatar tsaron ƙasar sun isa Yamai ranar Laraba domin bayar da horo ga dakarun tsaron Jamhuriyar Nijar, kamar yadda gidan talbijin na gwamnatin ƙasar RTN ya bayyana.
Wannan mataki wani ɓangare ne na kyautata danganta tsakanin mahukuntan Moscow da sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, kamar yadda mai watsa labaran da ya karanto wata sanarwa daga gwamnatin ƙasar ya bayyana ranar Alhamis da maraice.
Wani bidiyo da RTN ya watsa ya nuna yadda wani jirgin ɗaukar kaya na soji ya sauka a ƙasar inda mutane suka zagaye shi.
Sanarwar ta ce sojojin Rasha da sauran ƙwararrun kan aiki soji guda 100 ne suka isa Yamai "domin horar da dakarunmu" a wani ɓangare na yarjejeniyar da shugaban Rasha Vladimir Putin ya ƙulla da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar don inganta tsaron ƙasar.
"Mun iso nan ne domin horar da sojojin Nijar da kuma yauƙaƙa danganta tsakanin Rasha da Nijar," a cewar wani mutum sanye da kakakin sojin, wanda talbijin na RTN ya ce yana daga cikin masu bayar da horon.
Mutumin ya rufe kusan galibin fuskarsa a yayin da yake jawabi.
Kazalika RTN ya ce Rasha ta amince ta kafa wasu na'urorin kakkaɓo jiragen sama a ƙasar Nijar. "Daga yanzu sararin samaniyarmu zai samu kariya," a cewar mai watsa labaran.
Nijar ta ƙulla wannan dangantaka da Rasha ce wata guda bayan gwamnatin sojin ƙasar ta sanar da yanke duk wata hulɗa da ta danganci haɗin-kai ta fannin soji da ƙasar Amurka "nan-take", tare da umartar dakarunta su fice daga sansanonin soji biyu da aka kashe fiye da $100m wajen gina su.
Kafin haka, sojojin Nijar sun kori dakarun Faransa kimanin 1500 da kuma jakadan ƙasar bayan dangantaka ta yi tsami tsakaninsu sakamako juyin mulkin da sojojin suka yi wa gwamnatin farar-hula ta Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.