Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta bayyana cewa sojojin ƙasar sun kashe ‘yan ta’adda 2,245 a cikin wata uku a faɗin ƙasar.
Sojojin sun halaka ‘yan ta’addan ne a yaƙin da suke yi da ‘yan Boko Haram, da ISWAP da kuma ISIS/Daesh, kamar yadda Manjo Janar Edward Buba ya bayyana a wani taron manema labarai a ranar Juma’a.
A samamen da sojojin suka kai tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni, sojojin sun samu nasasar ceto mutum 1,993 waɗanda aka yi garkuwa da su a faɗin ƙasar, kamar yadda daraktan watsa labarai na rundunar tsaron ya tabbatar.
Sojojin sun bayyana cewa sun samu nasarar ƙwato makamai 2,783 da kuma harsasai masu ɗumbin yawa daga ‘yan ta’addan.
A sanarwar, sojojin sun bayyana cewa sun samu ‘yan ta’adda da iyalansu 4,582 waɗanda suka yi saranda ga jami’an tsaro.
A baya-bayan nan dai Nijeriya na fuskantar hare-hare daga wasu kungiyoyi masu ɗauke da makamai da suka haɗa da Boko Haram da ISWAP a yankuna daban-daban na kasar.
Duk da cewa akwai hukuncin kisa na yin garkuwa da mutane a Nijeriya, ana yawan samun satar kudin fansa.
Kungiyoyin da ke dauke da makamai na kai hari a kauyuka, makarantu da matafiya a sassan arewacin kasar, inda suke neman kudin fansa.