Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta da ke yaƙi da ta'addanci a yankunan Arewa maso Gabashin ƙasar sun yi nasarar kama wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Boko Haram biyu tare da cafke wasu da ake zargin suna samar wa ƙungiyar bayanai da kayan aiki a jihar Borno.
A wata sanarwar da daraktan hulda da jama'a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Talata, ya ce ''rundunar ta kuɓutar da wasu mutane da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a yankuna daban-daban a fadin Nijeriya tare da ƙwato kayayyakin da 'yan daba suka sace da sunan yin zanga-zanga a ƙasar.''
''An kama kwamandojin Boko Haram Yamode da Usman ne bayan da suka kutsa kai cikin sansanin ‘yan gudun hijira na garin Damasak da ke karamar hukumar Mobbar a jihar Borno a ranar Lahadi, 4 ga watan Agusta,'' in ji sanarwar.
Rundunar ta ce wadanda ake zargin, sun yi ikirarin kai ziyara wurin 'yan uwansu da ke sansanin, kana sun taɓa kai hare- hare kan sojoji a yankin.
Kazalika rundunar ta kama wani Malam Mustapha Isma'ila mai shekara 49 da kuma Malam Abdulmudallabi Haruna mai shekara 30 waɗanda ake zarginsu da samar wa mayakan Boko Haram kayan aiki tare da ceto wasu ƙananan yara biyu a yayin samamen da suka kai yankin, in ji sanarwar.
''A halin da ake ciki, mutum 50 da ake zargin ‘yan Boko Haram ne tare da iyalansu sun miƙa wuya ga sojojin da aka girke a kananan hukumomin Bama da Gwoza da kuma Dikwa.
A wani samame da aka yi a jihar Yobe a ranar 4 ga watan Agustan 2024, an kama wasu mayakan Boko Haram guda uku a kasuwar Gubio da ke karamar hukumar Gubio,'' a cewar sanarwar rundunar.
A binkicen farko da aka gudanar, waɗanda ake zargin sun tabbatar da cewa suna da hannu a ayyukan garkuwa da mutane da kuma fashi da makami a yakin baki ɗaya.
Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da babura biyu da kuma wayoyin hannu da dama.
Haka kuma a jihar Kogi da ke yankin Arewa maso tsakiyyar Nijeriya, dakarun Sojojin ƙasar sun kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a yankin Egbe da ke karamar hukumar Yagba, ''Mohammed Bello, wanda ake zargin ya kasance cikin jerin 'yan ta'addan da jami'an tsaro suke nema ruwa a jallo,'' in ji rundunar.
Kazalika, sanarwar ta ce ''a artabun da aka yi da 'yan ta'addan a wani hari da suka kai yayin garkuwa da tsohon shugaban karamar hukumar Kabba a yankin, dakarun sun kama ɗaya daga cikin yan ta'addan a dajin Egbe tare da kuɓutar da wanda aka yi garkuwa da shi kuma tuni aka sada shi da iyalansa.''