Hedikwatar ta faɗi hakan ne a wata sanarwa da a yau Alhamis ta bakin Daraktan Watsa Labaranta Manjo Janar Edward Buba. DHQ

Hedikwatar Rundunar Tsaron Nijeriya ta ce dakarunta sun daƙile wasu shirye-shirye na “’yan ta’adda” na lalata wasu muhimman abubuwan more rayuwa a ƙasar.

Hedikwatar ta faɗi hakan ne a wata sanarwa da a yau Alhamis ta bakin Daraktan Watsa Labaranta Manjo Janar Edward Buba, a wajen wani taron manema labarai da aka yi a Abuja.

Ta ce tuni ta ɗauki matakan tarwatsa wasu shirin “’yan ta’addar” ka iya sake yi, tare da ankarar da ukumomin tsaro don su tabbatar da kare muhimman ababen more rayuwa da kadarori na ƙasar.

Ya ce: “Sojoji suna fuskantar wasu muggan makiya da suke kokarin kashe ‘yan kasa ko kuma sun maa kashe ‘yan kasa. Hakika wadannan kungiyoyin ‘yan ta’adda su ne ke haddasa rashin tsaro a fadin kasar nan kuma ba za su daina yin abin da suke yi ba, har sai an daƙile su.

“Muna sane da wasu tsare-tsare na kai wa wasu muhimman ababen more rayuwa hari a kasar nan. Saboda haka, mun sanya matakan hana faruwar irin waɗannan shirin.

An kuma sanya hukumomin tsaro da ke da alhakin tabbatar da muhimman ababen more rayuwa da wurare a cikin shirin ko ta kwana. Saboda haka, wasu shirin na “mugaye” sun ci tura.

“A wannan fada, ’yan kasa su fahimci cewa ba za mu taba yin kasa a gwiwa ba a kan tsaro, idan ba haka ba lamarin tsaron kowa ka iya tabarbarewa. Wannan lamari ne da ba za a yi wasa da shi ba saboda mu rayu cikin aminci da tsaro.

“A halin yanzu, sojoji suna yin abin da ake bukata a wannan lokacin. Muna tilasta wa 'yan ta'adda girbar abin da suka shuka saboda ayyukansu na zalunci ga 'yan kasar nan. Mun gane kuma mun haɗa wannan a matsayin wani ɓangare na dabarunmu don cin nasara a yaƙin.

A ƙarshe ya ce rundunar soji ba ta da wani zaɓi illa fafutukar kare lafiya da tsaron ‘yan ƙasa.

TRT Afrika