Sojojin da suka yi juyin mulkin sun zargi ECOWAS da Farasana da yunkurin kawar da su daga kan mulki./:Hoto/Reuters

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun yanke huldar soji da ke tsakaninsu da makwabciyarsu Benin, suna masu zarginta da bari a yi amfani da kasar domin jibge sojoji da kayan yakin da ECOWAS za ta yi aiki da su don yiwuwar kai musu hari.

A wata sanarwa da sojojin suka karanta a gidan talabiji na kasar ranar Talata, sun ce Benin ta "bayar da umarni a yi amfani da sojoji da sojojin haya da kayan yaki" domin ECOWAS ta kai musu hari.

Don haka, sojojin na Nijar suka "yanke shawarar soke dangantaka da kawancen soji [da Benin]," in ji sanarwar.

Kawo yanzu Benin ba ta mayar da martani ba.

A karshen makon jiya sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suka yi zargin cewa Faransa tana tura sojojinta zuwa kasashen Yammacin Afirka da dama da zummar yin amfani da "kafin soji" a kansu.

Kakakin sojojin Kanar Amadou Abdramane ya yi ikirarin cewa ranar 1 ga watan Satumba Faransa ta tura jiragen soji biyu da kuma wani jirgi samfurin Dornier 328 domin karfafa dakarunta da ke Ivory Coast, yayin da kuma ta tura jiragen helikwafta biyu samfurin PUMA da motoci masu silke 40 zuwa Benin.

Labari mai alaka: Faransa ta tura dakarunta kasashen ECOWAS don shirin kai wa Nijar hari: Sojoji

Ya kara da cewa Faransa ta tura dakarunta kasashen da suka hada da Senegal, Benin da Ivory Coast, a wani bangare na ”shirin kaddamar da hari” a kan Nijar.

Ya zuwa wannan lokaci kasashen ba su ce komai kan zargin ba.

A makon da ya wuce Firaiministan Nijar Ali Mahaman Lamine Zeine ya ce sojojin suna tattaunawa da Faransa da zummar tabbatar da "gaggawar" kwashe dakarunta daga kasar.

Sai dai sojojin sun zargi Faransa da “rashin gaskiya da jan-kafa da kuma kafar-ungulu" don kawai ta kawar da su.

'Amfani da karfin soji'

Kungiyar ECOWAS ta sha alwashin yin amfani da karfin soji bayan da dakarun tsaron fadar shugaban Nijar suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli.

Sai dai ta ce za a yi hakan ne kawai idan dukkan hanyoyin diflomasiyya na rarrashin sojojin su mika mulki suka ci tura.

Amma sojojin sun ce za su mayar da martani mai karfi kuma nan-take kan duk wata kasa da ta nemi yi musu katsalantan ciki harkokin gidansu.

Sun samu goyon baya daga kasashen Mali da Burkina Faso da ke makwabtaka da su.

TRT Afrika