Hukumomin ƙasar Kongo za su gurfanar da akalla Sojoji 75 a ranar Litinin a kotu bisa samun su da laifin tsere dannawar da 'yan tawayen M23 ke yi gabashin yankin South Kivu da kuma cin zarafin fararen hula, ciki har da kisan kai da sace-sacen kayan jama'a, kamar yadda ofishin mai shigar da kara na rundunar sojin ƙasar ya sanar a ranar Lahadi.
Sojojin 75 waɗanda ke fuskantar shari'a, an tsare su sakamakon barin fagen dagarsu bayan kwace yankin Nyabibwe.
Ana tuhumarsu bisa laifin fyaɗe da kisa da ƙwace da tayar da zaune tsaye, kamar yadda ofishin mai shigar da kara na sojojin ƙasar ya shaida wa kamafanin dillancin labarai na Reuters.
Kazalika wasu da aka kama da irin wannan zargin, ana sa ran za su fuskanci shari'a, in ji ofishin.
Mai magana da yawun rundunar sojin Nestor Mavudisa ya ce, za a hukunta baragurbin sojojin kana ya yi ƙira ga jama'a da su kwantar da hankulansu.
Cin zarafin da dama
Majalisar Dinkin Duniya ta tattara rahoton bayanan cin zarafi da dama waɗanda suka hada da kisan gilla, da gungun fyade, da bautarwa ta hanyar lalata, biyo bayan mumunar farmakin ƙungiyar M23 a ƙarshen watan Janairu wanda ya kai ga ƙwace birnin Goma mafi girma a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo.
Mayakan M23, sojojin Kongo, da kuma mayakan sa-kai masu goyon bayan gwamnati duk suna da hannu a take hakkin bil adama, a cewar ratohon ofishin MDD..
DRC dai ba ta ce uffan ba game da rahotannin da suka shafi sojojinta amma ta yi ƙira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta gudanar da bincike kan take hakkin da ta ɗora wa 'yan tawayen M23 da ƙasar Rwanda.
Rwanda, wacce ta musanta mara wa ƙungiyar baya, ta yi watsi da ɗaukar duk wani nauyi.
Kazalika 'yan tawayen na M23 ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba.
Faɗaɗa ayyukan tawaye
Duk da sanarwar tsagaita wuta da ta yi, 'yan tawayen ƙungiyar M23 na ci gaba da kutsa kai yankin Kudu zuwa babban birnin South Kivu da Bukavu.
A makon jiya ne, sun kwace iko da garin Nyabibwe, mai tazarar kilomita 70 daga arewacin babban birnin lardin.